An yi Kira ga hukumar zaben Najeriya da ta gaggauta sanar da sakamakon zaben jihar Adamawa maimakon sake gudanar da zabe a wasu mazabu. Wannan Kira ya fito ne daga bakin mataimakiyar shugabar mata na jam’iyyar APC dake kula da shiyyar Arewa maso gabas Honorobul Zainab Abubakar Ibrahim a daidai lokacin da al’umar Najeriya ke cigaba da tofa albarkacin bakunansu dangane zaben gwamnoni da na yan Majalisun dokokin jihohin kasar.
Kazalika, ta bukaci masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye domin kare Martaban Demokuradiyya a fadin kasar dama wasu kasashen Afirika ta hanyar sanar da sakamakon zaben jihar Adamawa maimakon sauya zaben wasu mazabu kamar yadda hukumar zaben Najeriya Mai zaman kanta INEC ta sanar da zaben a matsayin wanda ba a kammala ba, wato inconclusive a turance.
Mataimakiyar shugabar mata na jam’iyyar APC Mai mulkin Najeriya ta ci gaba da cewa ” Tun jiya kowa ya san Sanata Aishatu Dahiru Binani ce ta ci wannan zaben na Gwamna a Adamawa mutane har sun fara buki suna murna amma aka ki sanar da sakamakon zaben nan akan lokaci domin akwai lauje cikin Nadi Kasan an cigaba Kai tsaye zaben nan ke zuwa ga rumbun tattara bayanai na INEC sakamakon yin amfani da na’urar VBAS don haka mu mata muna tare da ita Kuma muna jinjina mata”
Bugu da Kari, Yar siysar ta jaddada Kira ga hukumar zaben Najeriya da ta yi amfani da kundin tsari mulkin Najeriya da ya yi gyaran zabe a sashi na 65 wanda ya baiwa INEC dama ta gyara kurarenta cikin kwanaki bakwai wajen ganin ta sanar da zaben ba tare da wata wata ba.
A cewar ta bata shakka idan za a yi zabe sau Dari, Sanata Binani za ta ci zaben sau Dari Amma basa bukatar sake zabe ko zuwa kotu saboda wannan duk bata lokaci ne.
A karshe ta bukaci daukacin matan Najeriya da su kara hakuri da juriya domin ganin an baiwa abunda al’umar Adamawa suka zaba.
AK
Leave a Reply