Take a fresh look at your lifestyle.

SHARE HAWAYEN TALAKA SHI MUKA SA GABA…ABBA GIDA-GIDA

Yusuf Bala Nayaya,Kano.

0 388

Zababben gwamnan jihar ta Kano Arewa maso Yammacin Najeriya Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida) na jam’iyyar NNPP ya rantsar da kwamiti da zai yi aikin karbar mulkin Kano daga gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC. Kwamitin mai mambobi 65 zai yi aiki ne karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Baffa Bichi da ke zama tsohon shugaban Asusun kula da Ilimin manyan Makarantu a Tarayyar Najeriya TETFUND kuma tsohon dantakarar sanata a Kano ta Arewa.

 

 

A lokacin da yake rantsar da mambobin kwamitin na GTC a otel din Tahir Guest Palace da ke Kano, zababben gwamnan ya ce gwamnatin da suke muradun kafawa gwamnati ce da za ta mayar da hankali wajen samar da cigaba da share hawayen talakawa da gyara barnar da aka aikata don samun waraka. Don haka cikin ayyuka da ake tsammanin kwamitin ya gudanar sun hadar da tattara bayanai na yadda aka gudanar da gwamnati mai baring ado da bayanan halin da jaha ke ciki da yadda bangaren zartarwa ya gudanar da aiki ta yadda sabuwar gwamnati za ta samu damar fara gudanar da aikinta cikin nasara.

 

 

Yace yana tsammanin mambobin kwamitin za su nuna kwarewarsu  da aiki tukuru da gaskiya da nuna kishin kasa yayin gudanar da aikin da zai zama danba ta samar da zaman lafiya mai dorewa da bunkasar tattalin arziki da ci gaba a jihar ta Kano.

 

 

Da yake mayar da martani amadadin mambobin kwamitin Dakta Bichi ya ce za su yi aiki tukuru don tabbatar da ganin sun cimma nasara kan wannan aiki da aka basu. Ya kuma gode wa zababben gwamnan saboda yadda ya amince da su a matsayin wadanda za su gudanar da wannan aiki mai muhimmanci ga jihar ta Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *