Take a fresh look at your lifestyle.

Easter: – Gwamnan Yobe Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Yi Addu’ar Samun Zaman Lafiya

0 154

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da bikin Ista wajen yin addu’o’in mika mulki cikin nasara da lumana a daidai lokacin da Najeriya ke shirin samun sauyin shugabanci.

 

 

Gwamna Buni ya bayyana hakan ne a cikin sakon fatan alheri ga mabiya addinin Kirista na bikin Easter.

 

 

A cewarsa, yana da matukar muhimmanci a sanya dabi’un soyayya da sadaukarwa kamar yadda koyarwar Easter ke nunawa a wannan lokaci na rayuwarmu ta kasa.

 

 

“Ya kamata a yi amfani da kyawawan darussan soyayya da sadaukarwa don inganta zaman lafiya da hadin kai don ci gaban kasa da ‘yan Najeriya,” in ji shi.

 

 

 

Gwamnan ya bayyana cewa wannan lokaci ne mai albarka da mabiya addinin kirista ke gudanar da bukukuwan Easter a daidai lokacin da ‘yan uwansu musulmi ke gudanar da azumin watan Ramadan.

 

 

“Don haka babbar dama ce a gare mu a matsayinmu na kasa mu yi amfani da wannan lokacin wajen yi wa kasarmu addu’a.”

 

Gwamnan ya yi kira ga shugabannin addini da na al’umma da su zauna tare cikin lumana.

 

 

Za mu iya yin addininmu kuma mu sami ci gaba idan muka sami zaman lafiya.

 

 

“A wasu shekarun baya, ba mu iya zuwa masallatai da coci-coci a jihar Yobe saboda kalubalen tsaro, amma a yau mun gode wa Allah domin zaman lafiya da muke samu a fadin jihar.

 

 

“Don haka ya kamata mu kiyaye ta da kishi kuma mu guji duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya da tsaro a jihar Yobe da Najeriya,” in ji shi.

 

 

Aisha Yahaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *