Miliyoyin Musulmi Da Kirista A Jahar Kaduna Sun Yi Azumi Don Neman Saukin Matsalar Tsaro
Abdulkarim Rabiu, Kaduna
Sama da al’ummar Jihar Kaduna Musulmi da Kirista miliyan biyar ne suka tashi da Azumi na musanman domin neman sauki daga Ubangi agame da matsalar tsaro da kuncin rayuwa dake ci gada da addabar wasu sassa na Jihar da kuma bukatar tabbatuwar sahihiyar Demokradiyya’
An dai gudanar da Azumin ne a ciki da wajen Jihar domin neman daukin Ubangiji dangane da yanayin halin rayuwa da al’ummar Jihar su ke ciki.
Azumin wanda ya gudana a ranar litinin sakamakon wani kira da Dan takarar Kujerar Gwamnan Jihar Kaduna, a karkashin Jam’iyyar APC, Honarabul Sani Sha’aban ya yi, inda aka gudanar da taron bude baki na shan ruwan Azumin wanda ya samu halartar akalla sama da Fastoci 30 da wasu manyan malaman Addinin Musulunci a ofishin kamfen na dan takarar dake garin Kaduna.
Da yake jawabi a wajen taron bude bakin Azumin, Dan takarar kuma Danburan Zazzau Sani Sha’aban, ya bayyana cewa wannan wani mataki ne da suka dauka domin neman kawo karshen halin ha’ula’i da al’ummar Jihar ke ciki sakamakon irin yadda al’amura na rashin kwanciyar hankali suke kasancewa.
Ya kara da cewa al’ummar Jihar basu da wani karfi wanda ya wuci karfin Ubangiji kuma a dalilin hakan ne suka gudanar da wannan Azumin na musamman domin neman samun sauki a cikin rayuwar su da al’amuran Jihar Kaduna wanda hakan ke neman salwantar da rayuwar al’ummar.
Ya ce “Ni mutumin Zariya ne kuma daga Zariya na Fito, kuma yanzu haka akalla sama da mutane Miliyan daya suka gudanar da wannan Azumin wanda mu ka yi bude baki a nan cikin cikin garin Kaduna.”
“Kuma a cikin garin Kaduna akalla sama da mutane Miliyan daya suka gudanar da wannan Azumin, haka a garin Zankuwa, Kafanchan da Kachia kuma muna saran Allah Zai dubi al’amuran mu ta hanyar da zamu samu saukin rayuwa”.
Acewarsa, wasu da dama daga cikin al’ummar Jihar sun rasa ayyukan su, a yayin da wasu matasa suka kasa yin karatu sakamakon karin kudin makaranta wanda hakan yasa iyayensu basa iya biyan kudin makarantarsu.
Dan takarar Kujerar Gwamnan, ya ci gaba da cewa akalla kusan kwanaki casa’in kenan da aka yi garkuwa wasu al’umomin Jihar Kaduna a harin Jirgin Kasa, to amma har yanzu Gwamnatin ta kasa yin komai domin ganin an sako su.
Honarabul Sha’aban, ya kara da cewa ya shigar da kara kotu domin neman hakkin shi a bisa karfa-karfan da aka yi masa a lokacin zaben fidda gwani na Jam’iyyar ta APC, kana ya aika da sakon neman ita Uwar Jam’iyyar ta dauki matakin da ya dace na ganin cewa ta daidaita al’amura a tsakanin duka Ya’yan Jam’iyyar.
ZABEN FIDDA GWAMAN
Dan gane da batun zaben fidda gwani da Jamiyyar APC ta gudanar a jihar kuwa, Sani Sha’aban ya yi nuni da cewa masu zaben yan takara wato (deliget) 1224 da suka sayi fom din zama masu zaben yan takara ba a basu dama ba, su ma sun shigar da kara kotu domin neman hakkin u bisa rashin adalcin da aka yi musu da tauye musu hakki a lokacin zaben.
A karshe, Barden Keffi Sani Sha’aban, ya bayyana cewa suna sa ran wannan Azumin da suka gudanar kuma su kayi tawassali da shi, zai zame musu wata silla na samun waraka bisa duk wata damuwar da ta addabe su a ciki da wajen Jihar ta Kaduna.
An dai gudanar dai gudanar da taron buda bakin ne a tsakanin al’ummar Musulmi da Kirista da ke duka kananan hukumomin 24 dake daukacin jihar ta Kaduna.
Ga Rahoton da Abdulkarim Rabiu ya hada mana daga Kaduna:
Abdulkarim Rabiu
Leave a Reply