A jajiberin barinsa aikin dansanda kwamishinan ‘yansandan jihar ta Kano CP Mamman Dauda, da yayi aikin na dansanda a matakai daban-daban tun daga mataki na SP a kuma jihohi daban-daban da suka hada da jihar Kano da ya zo a matsayin kwamishinan ‘yansanda a ranar 10 ga watan Nuwamba shekarar 2022. Yayi aiki a matakai daban-daban a jihar Borno da Zamfara da Kaduna da Nasarawa da Gombe da Katsina da Kano dai sauransu.
Da yake jawabi ga ‘yansandan da sauran masu ruwa da tsaki a babban dakin taron na ‘yansanda da ke a Miller Road Bompai a jajiberin barinsa aiki CP Mamman Dauda ya ce tafiya ce ba mai sauki ba amma da taimakon Allah ya kai ga wannan matsayi kuma nasarar da ya cimma kawo yanzu ta samu ne saboda irin tallafi da ya samu daga babban sifeton ‘yansanda na kasa Usman Alkali Baba da Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje wanda yace duk bukatar da suka gabatar a gare shi yana basu kulawar da ta dace.
“Bukatu da muke da su idan muka gaya masa ,yana bamu goyon baya don mu tabbatar da nasara a aikin mu tabbatar da ganin cewa Kano tana zaune lafiya. Sannan akwai MD na KAROTA da shugaban PCRC da Alhaji Nasidi da Sanata Barau da Alhaji Ibrahim Gerawa da shugaban kungiyar ‘yan jarida ta NUJ da Aminu Magashi da uwar marayu da dai sauran. Na ga cewa bai yi kyau ba idan har nagama aiki nay i nasara ban je nace masu nagode ba, na yi butulci. Shi ya san a tsakuro kadan daga cikinsu don nace nagode maku. ”
Kwamishina Dauda ya kuma yaba wa kwamandoji da suka mara masa baya don cimma nasarar da yayi wadanda yace ba don su ba da bai kai ga wannan mataki ba da ya kai jihar ta Kano da samun zaman lafiya.
“Duk da zaben da aka yi a Kano ana zaune lafiya, batu na ace babu tashin hankali ko yaya bamu kai nan ba amma gashi an yi zaben an kammala jihar na zaune lafiya mun gode Allah duk wannan nasara da aka cimma ta samu dalilin gudunmawa da kuke bayarwa ce. Saboda haka ina maku godiya Allah Ya saka maku da alkhairi. Muna cikin watan Azumi duk ibadun da muka yi Allah Ya karba, wadanda suka je Umrah Allah Ya dawo da su lafiya. Ina maku godiya ta musamman haka jami’in hulda da jama’a na ‘yansanda ina godiya”
Kafin dai bikin bankwanar sai da kwamishinan ‘yansandan jihar ta Kano amadadin sifeto janar na ‘yansanda ya kaddamar da bude sabbin gidaje 88 na ‘yansanda a bangaren shelkwatar ‘yansandan da ke Bompai a wani bangare na gina gidaje sama da 200 da za a yi a wannan waje.
Leave a Reply