Take a fresh look at your lifestyle.

SHUGABAN NAJERIYA YAYI KIRA GA MALAMAN JAMIO’I DA SU JANYE YAJIN AIKI

0 352

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi kira ga kungiyar Malaman Jamioii na Najeriya ASUU da su sake duba matsayin su akan yajin aiki day a dauki tsawon lokaci,ya lura da cewa hakan wani abun damuwa ne dake barazana ga iyalai ,ilimi da ci gaban kasa.

Shugaban wanda ya karbi bakuncin Gwamnonin Jamiyyar All Progressives Congress (APC), ‘Yan Majalisu da shugabannin siyasa a gidan shi dakeDaura, Jihar Katsina ranar Litinin, yace wannan yajin aiki ya sanya wa Iyaye,Dalibai da sauran masu ruwa da tsaki tare da watsi da dukl abubuwan da aka riga aka roke su akai.

Muna fatan cewa ASUU zata tausayawa jama’a akan yajin aiki,gaskiya lokaci yayi da Dalibai zasu daina zaman dirshe a gidajen su. Don Allah Kada ku bata rayuwar al’uma nan gaba,” a cewar shi.

 

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *