Take a fresh look at your lifestyle.

An Kusa Kammala Ginin Ofishin NASC Na Dundundun: Injiniya Amshi

Musa Aminu, Abuja

0 209

Hukumar dake kula da ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya wato National Assembly Service Commission a turance, ta sha alwashin kammala ginin ofishinta na din-din cikin wannan shekarar da muke ciki.

Shugaban hukumar Injiniya Ahmed Amshi shi ne ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da Muryar Najeriya dangane da waiwayen nasarorin da hukumar ta samu a shekaru da yayi yana jan ragamar hukumar.

Injiniya Amshi ya bayyana cewa tun bayan da ya fara aiki gadan-gadan a shekarar 2020 abu na farko da ya fara yi shi ne zama da ma’akaitan hukumar domin fahimtar matsaloli da suke ciki ta yadda zasu fuskance su gadan-gadan da nufin magance su.

To sai dai kuma da dama daga cikin al’umma basu san nauyin da ya rataya a wuyan hukumar ba, wanda a cewarsa ayyukan da doka ta sahalema wa hukumar sun hada da samar da kwararrun ma’aikta da zasu taimaka wa yan majalisar dattawa da na wakilan tarayya da kuma nada akawun majalisa da wadanda zasu taimaka masa gudanar da aiki a matsayin mataimaka, sai nada manyan sakatarori dake kula da majalisa, akwai kuma  daga darajar ma’aikata da ma hukunta duk wani ko wata da su ka yi ba daidai yayin gudanar da aiki.

Sauran sun hada da horas da ma’aikata domin sake samun kwarewar aiki  da dai sauransu.

A cewar shugaban hukumar dake kula da ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya, kawo yanzu sun sami nasarori kamar haka;

“Mun shirya tsarin aiki wanda ko wane ma’aikaci zai ji dadin aiki a majalisar dokoki. Bayan haka kuma mun yi wasu tsare- tsare na gyara halayen ma’aikatan kansu, mu tabbata cewa suna tafiyar da aikinsu a cikin ofis yadda ya kamata cikin da’a, sannan mun kaddamar da littafi akai kuma ko wane ma’aikaci an ba shi. Mun kuma fadada ita ma’aikartar majalisar gaba daya, mun kirkiri  sashe-sashe wadanda ma’aikata za su sami ci gaba domin a sami daraktoci da dama kowa ya samu abin yi”. In ji injiniya Amshi

Ya kara da cewa “mun tabbatar an biya ma’aikata alawus alawus da suke bin bashi tun da dadewa. A zuwamnu mun samu an dauki ma’aikata wajen 221, an basu wasiku, an basu komai saura su fara aiki kawai sai yan majalisar dokoki suka ki daukar su aiki. Da muka yi nazari muka ga ba a kyauta musu ba sai muka roki shugabancin majalisa suka bamu izni duka muka dauke su”

Kazalika, ya kara da cewa kimanin ma’aikata 2745 yanzu haka an  kara masu girma a wajen aikinsu wanda hakan ya kara masu kuzarin gudanar da ayyukansu na yau da kullum, sai dai kuma duk da irin wannan nasarori da hukumar ta samu cikin shekaru uku, a shekarar da ta gabata ma’aikatan majalisar sun rika gudanar da zanga-zanga dangane da mukamin akawun majalisar, abunda shugaban ma’aikatan ya danganta da rashin fahimta ne ya haifar da haka.

“Kwata-kwata al’amarin nan babu rudani, rashin fahinta ne ya haifar da hakan, abin da ya faru akawun majalisa ne lokacin ritayarsa ya yi, mun nada wani, nadawar kuma a kwai ka’idodi kamar yadda kundin tsarinmu ya nuna mana, mun bi wadannan ka’idodi  abin da dokar tsarin mulkinmu na hukuma ya gaya mana. Wadansu dai bai musu dadi ba shi ne suka yi ta wannan hayaniya. Mu a ganinmu babu wani rudani, mun yi aikinmu yadda doka ta tsara”.

A cewar Injiniya Ahmed Amshi babban nasarar da suka samu shi ne na gina ofis na din-din ga maai’katar hukumar wanda yanzu haka an kamala kaso saba’in da biyar zuwa tamanin, sai dai ya bayyana karancin masu ruwan rana a matsayin abunda ke kawo masu tsaikon gudanar da ayyukan da suka sanya a gaba.

Ga Musa Aminu Dauke da Cikakken Rahoto akan haka: dan nan ka saurara

AMSHI REPORT

Abdulkarim Rabiu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *