An ji harbe-harbe da fashewar abubuwa a duk fadin birnin Khartoum na kasar Sudan a rana ta 20 a jere.
Shaidu sun ba da rahoton karar fashewar abubuwa da kuma musayar wuta a kan tituna.
An kuma yi tashin bama-bamai masu yawa a garuruwan Omdurman da Bahri da ke makwabtaka da su.
Rundunar ta ce a shirye ta ke ta yi biyayya ga sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta kwanaki bakwai, amma babu wata sanarwa daga bangaren ‘yan sandan da ke fafutuka, Rapid Support Forces (RSF).
Sojojin sun ce sun kashe mayakan RSF tare da lalata wasu motoci “na ‘yan tawayen”, bayan sun yi arangama da kungiyar a yankin sojojin na Bahri.
Rahotanni sun ce ana kokarin korar dakarun RSF daga yankin da ke kusa da fadar shugaban kasa da kuma hedkwatar sojoji.
Babban jami’in bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths, ya ce matakin da bangarorin da ke fada da juna suka dauka na ci gaba da fada yana cikin kasadar mayar da rikicin zuwa wani bala’i a duniya.
Leave a Reply