Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ta kaddamar da kwamitin mika mulki da zai gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar masu zuwa a jihar Ebonyi.
Taron wanda ya gudana a Abakaliki babban birnin jihar ya kawo Farfesa Sunday Opoke a matsayin shugaba.
Shugaban kwamitin, Ogbonnia Oko Enyim, ya ce ma’anar kwamitin mika mulki shi ne tabbatar da zaben sabbin shugabannin jam’iyyar ADC cikin kwanciyar hankali da lumana.
“Zamanin zama a jam’iyyar da yiwa jam’iyyar zagon kasa ya wuce, idan kun san cewa ba ku na ADC ba, ku girmama kanku ku bar zaman lafiya,” in ji shi.
Sabon shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar ADC Sunday Opoke, ya ce jam’iyyar na shirin sauya kasar zuwa abin da ‘yan Najeriya ke bukata.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ADC za ta gyara kasar nan domin amfanar dukkan bil’adama.
Ya kara da cewa “Jam’iyyar mu, ADC za ta baiwa dukkan ‘yan Najeriya abin da ake kira kyakkyawan shugabanci.”
Shugaban kungiyar hadin kan kasa a jihar Kenneth Oziomaeze ya ce ADC ta zo ne domin ta samar da irin shugabancin da ‘yan Najeriya ke so.
Daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar ADC a jihar, Solomon Adum, ya bukaci al’ummar Ebonyi da su hada kai da jam’iyyar domin ganin an samu nasara a 2027.
Shugabar Mata ta Jam’iyyar, Misis Lilian Nwankwo, ta ce lokaci ya yi da za a yi taro na gari.
Taken bikin kaddamarwar shi ne “Sake matsayi na Ebonyi don Jagorancin Jama’a.”
Aisha. Yahaya, Lagos