Kawayen Turai da Canada sun ba da biliyoyin daloli don tallafa wa Ukraine tare da amincewa da kara yawan kudaden da ake kashewa a fannin tsaro don karfafa tsaron nasu.
Duk da haka, haɗin kai da amincin NATO ya yi matukar tabarbarewa a cikin shekarar da ta gabata saboda karuwar tashe-tashen hankula na cikin gida, musamman abin da ya shafi Amurka.
Rikicin dai ya kara kamari ne bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya sha ba da shawarar kwace yankin Greenland, wani yanki mai cin gashin kansa na kasar Denmark memban kungiyar tsaro ta NATO, sannan ya yi kalaman batanci game da sojojin kawancen da suka yi yaki tare da sojojin Amurka a Afghanistan.
Masu sharhi sun ce wadannan ayyuka sun raunana amincewa a cikin kawancen membobi 32 da kuma raunana karfin NATO na dakile Rasha. Kodayake mambobin NATO sun yi alkawari a watan Yuli don haɓaka kudaden tsaro zuwa kashi 5 cikin 100 na GDP nan da 2035, damuwa ya kasance cewa rarrabuwar siyasa musamman shakku game da sadaukar da kai ga Amurka ga tsaron gama gari a ƙarƙashin Mataki na 5 – sun ƙarfafa abokan gaba.
Rasha ta fito fili ta yi tsokaci game da rikicin cikin gida na kungiyar tsaro ta NATO, yayin da jami’an Turai ke gargadin cewa Moscow na ci gaba da zama barazana ta tsaro na dogon lokaci.
Rahotanni na hare-haren yanar gizo, zagon kasa, da kuma tsoratar da sojoji a duk fadin Turai sun kara wannan damuwa.
Rashin tabbas kan yuwuwar rage sojojin Amurka a Turai ya kara girgiza kwarin gwiwa kan matakin da kungiyar tsaro ta NATO ke dauka.
Yayin da ministocin tsaro na NATO ke shirin ganawa nan gaba a wannan watan, manazarta sun yi gargadin cewa idan ba tare da dawo da hadin kai da fayyace manufa ba, karfin kungiyar na iya yin rauni sosai ga barazanar da ake fuskanta a nan gaba.
Aisha. Yahaya, Lagos