Amurka da Iran sun kasa cimma matsaya, biyo bayan tattaunawar gudun fanfalaki da aka gudanar a birnin Islamabad na Pakistan a ranar Lahadin da ta gabata, inda aka kawo karshen kokarin da ake na rage takun saka tsakanin kasashen biyu.
Tattaunawar ta sa’o’i 21, an kammala ba tare da cimma matsaya ba, inda bangarorin biyu suka yi nuni da cewa, an samu babban rashin jituwa kan shirin nukiliyar Iran da kuma matsalar tsaron yankin baki daya.
Majiyoyin diflomasiyya sun ce tattaunawar, wacce ta biyo bayan shirin tsagaita bude wuta na baya-bayan nan, ta kare ne ba tare da cimma wata nasara ba, lamarin da ya sanya ayar tambaya kan dorewar rashin fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu.
Wani babban jami’in Amurka ya ce Washington ta fito fili ta bayyana matsayinta yayin tattaunawar.
Jami’in ya ce “Mun fito fili karara menene jajayen layukanmu; ba mu cimma matsaya ba, kuma hakan yana nuni da matakin da Iran ta dauka na kin amincewa da sharuddan da ke kan teburin.”
Amurka ta dage cewa dole ne Iran ta ba da tabbacin cewa ba za ta ci gaba da yin amfani da makaman nukiliya ba ko kuma samar da fasahohin da za su iya ba da damar yin amfani da makamai cikin gaggawa.
Jami’in ya ce “Muna bukatar ganin wata kwakkwarar alkawarin cewa ba za su nemi makamin nukiliya ba kuma ba za su samar da kayan aikin da zai ba su damar cimma daya cikin gaggawa ba.”
Jami’an Iran, a cewar kafofin yada labarai masu alaka da gwamnati, sun bayyana bukatun Amurka da wuce gona da iri. Jami’an Iran sun amince da wasu ci gaba kan wasu batutuwa, amma an ci gaba da samun gagarumin bambance-bambance dangane da shirin nukiliyar Iran da mashigin Hormuz.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya ce an gudanar da tattaunawar cikin yanayi na rashin yarda da juna, inda ya kara da cewa ba gaskiya ba ne a yi tsammanin cimma cikakkiyar yarjejeniya a zagaye guda na shawarwarin.
Ministan harkokin wajen Pakistan, Ishaq Dar, ya ce yana da muhimmanci a kiyaye tsarin tsagaita wuta a halin yanzu yayin da ake ci gaba da kokarin diflomasiyya.
Rahotanni sun nuna cewa tattaunawar da aka yi a Islamabad ita ce ta farko kai tsaye tsakanin Amurka da Iran cikin shekaru goma.
Tuni dai tawagogin biyu suka koma kasashensu, a cewar majiyoyin diflomasiyya.
Reuters/A’isha.Yahaya, Lagos