Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Kano Ya Raba Tallafin Jarin Fara Aiki Ga Mata

218

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya raba Naira 50,000 kowannen su a matsayin jarin fara aiki ga daruruwan mata a karkashin shirin tallafawa da Talauci na jihar na wata-wata da nufin karfafa kananan sana’o’i da inganta rayuwa.

 

An bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature.

 

Da yake jawabi yayin kaddamar da shirin raba kudaden na shekarar 2026 a gidan gwamnati Gwamna Yusuf ya ce da gangan an tsara shirin ne domin baiwa wadanda suka ci gajiyar tallafin ba da gudummawa mai ma’ana ga tattalin arzikin kananan hukumomi.

 

Ya bayyana cewa shirin rage radadin talauci yana wakiltar cika alkawuran yakin neman zabe da gwamnatinsa ta yi wa al’ummar jihar Kano inda ya kara da cewa an ware shekarar 2026 a matsayin shekarar karfafa gwiwar maza da mata da matasa.

 

A cewar Gwamnan an fara aiwatar da shirin tun bayan hawanshi mulki inda dubban mata suka amfana tare da samun ci gaba mai ma’ana a yanayin rayuwarsu.

 

Da yake karin haske kan tasirin shirin Yusuf ya bayyana cewa daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin ta zuba tallafin da ta fara bayarwa na Naira 50,000 a harkar kasuwanci kuma ta yi nasarar bunkasa shi zuwa sama da Naira miliyan 1.2 cikin shekaru biyu.

 

Ya bukaci sabbin wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da kudaden don tallafawa iyalansu da kuma bayar da gudumawa mai kyau ga al’ummarsu.

 

Gwamnan ya kuma yabawa majalisar dokokin jihar Kano karkashin jagorancin kakakin majalisar Jibril Falgore da kuma shuwagabannin kananan hukumomi 44 bisa goyon bayan da majalisar ta basu da kuma fitar da kudaden shirin a kan lokaci.

 

A nasa jawabin shugaban majalisar Falgore, ya ce irin ayyukan raya ababen more rayuwa da ayyukan rage radadin talauci da gwamnatin Yusuf ke aiwatarwa ya bayyana a fadin jihar yana mai cewa hatta masu suka sun yarda da irin tasirin da gwamnatin ke da shi.

 

Tun da farko da yake magana a madadin kungiyar kananan hukumomin Najeriya (ALGON) shugaban karamar hukumar Danbatta Jamilu Dambatta wanda ya wakilci shugabar hukumar Hajiya Sa’adatu Soja ya yaba wa gwamnan bisa tsarin jagoranci da ya hada da jama’a.

 

Comments are closed.