Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnoni Za Su Mika Tsarin ‘Yan sandan Jihohi Ga Majalisar Dokoki Ta Kasa

46

Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta ce nan ba da jimawa ba za a mika cikakken tsarin kafa ‘yan sandan jihohi ga Majalisar Dokoki ta kasa a wani bangare na sabbin tsare-tsare da hadin kai na magance kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman AbdulRazaq ne ya bayyana hakan a lokacin bikin Sallah da gwamnoni 25 suka kai wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a gidansa na Ikoyi da ke Legas ranar Lahadi da ta gabata.

Gwamnonin sun kuma yi alkawarin karfafa hadin gwiwa da kokarin shawo kan matsalar rashin tsaro, tare da ciyar da ci gaban samar da ababen more rayuwa da inganta zamantakewa da tattalin arziki ga ‘yan kasa, bisa la’akari da manyan tsare-tsare na gwamnati.

“A game da batun ‘yan sandan jihohi, ana ci gaba da tattaunawa a tsakanin kungiyoyin tsaro daban-daban, karkashin jagorancin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, kuma NGF ta bayar da gudunmawarta, za a kai wannan takarda ga majalisar dokokin kasar domin ganin yadda za mu samar da tsarin doka ga ‘yan sandan jiha.

Mun himmatu wajen sabunta haɗin gwiwarmu da jami’an tsaro don murkushe ta’addanci, don ci gaba da faɗaɗa hanyoyin samar da ababen more rayuwa, da inganta rayuwar al’ummarmu. A tare, dole ne mu ga an kawo karshen matsalar tsaro a duk fadin kasar.”

Shugaban na NGF ya kuma yabawa shugaba Tinubu kan aiwatar da ajandar sabunta bege, wanda ya ce ya kara zurfafa tunanin ‘yan kasa na shiga cikin ci gaban kasa tare da yin alkawarin inganta tsaro.

A cewarsa, kokarin hadin gwiwar shugabanni a dukkan matakai, wadanda suka danganci hadin kai, tausayawa, da kuma daukar nauyi, na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen samun dawwamammen zaman lafiya da wadata.Ya jaddada cewa,

Ziyarar wacce ta samu halartar gwamnoni 25 daga sassan tarayyar kasar, ta jaddada abin da AbdulRazaq ya bayyana a matsayin hadin kai da goyon baya ga shugabancin shugaban kasar.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Sen. Hope Uzodinma, jihar Imo; Alex Otti, Jihar Abia; Umo Eno, Jihar Akwa Ibom; Douye Diri, Jihar Bayelsa; Hyacinth Alia, Jihar Benue; Bassey Otu, Jihar Kuros Riba; Sheriff Oborevwori,r Jihar Delta; Francis Nwifuru, Jihar Ebonyi; Monday Okpebolo, Jihar Edo; Peter Mbah, Jihar Enugu; Mohammed Inuwa Yahaya, Jihar Gombe; da Umar Namadi, Jihar Jigawa.

Sauran: Abba Kabir Yusuf, Jihar Kano; Dikko Umaru Radda, Jihar Katsina; Ahmed Usman Ododo, Jihar Kogi; Babajide Sanwo-Olu, Jihar Legas; Abdullahi Sule, Jihar Nasarawa; Caleb Mufwang, Jihar Filato; Siminalayi Fubara, Jihar Ribas; Agbu Keffas, Jihar Taraba; Mai Mala Buni, Jihar Yobe; da Lucky Aiyedatiwa, Jihar Ondo.

Mataimakin gwamnan jihar Borno Umar Usman Kadafur shi ma ya halarci taron

 

A’isha. Yahaya Lagos

 

Comments are closed.