Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya ce tawagar ma’aikatanta sun tattauna da jami’an kasar Gabon kan yanayin tattalin arzikin kasar da kuma alkiblar manufofin kasar.
A cewar IMF, tattaunawar ta mayar da hankali kan ci gaban tattalin arziki na baya-bayan nan da kuma tsare-tsaren gwamnati na inganta ci gaban tattalin arziki.
Jami’ai daga bangarorin biyu sun kuma tattauna kan matakan da suka dace na karfafa tattalin arzikin kasar da kuma tallafawa ci gaba mai dorewa.
A yayin tarukan, an mai da hankali kan sauye-sauyen da ake gudanarwa domin inganta harkokin tafiyar da kudaden gwamnati da kuma karfafa harkokin mulki.
IMF ta ce, “waɗannan gyare-gyaren suna da mahimmanci don tabbatar da gaskiya, inganci da ingantaccen amfani da dukiyar jama’a”.
Tattaunawar ta kuma jaddada muhimmancin kiyaye tsare-tsare na kasafin kudi.
IMF ta yi nuni da cewa, irin wadannan matakan sun zama wajibi domin kare daidaiton tattalin arziki a Gabon da ma fadin yankin baki daya.
Asusun ya ce zai ci gaba da yin aiki kafada da kafada da hukumomin kasar Gabon yayin da suke gudanar da sauye-sauye da manufofin da ke da nufin tallafawa ci gaba mai dorewa da kuma wanzar da kwanciyar hankali a fannin tattalin arziki.
Reuters/A’isha.Yahaya,Lagos