Majalisar dokokin Kamaru a ranar Asabara Da ta gabata, ta amince da gyaran kundin tsarin mulkin kasar wanda ya samar da mukamin mataimakin shugaban kasa, duk da kakkausar suka daga ‘yan adawa.
‘Yan majalisa 200 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudirin, yayin da 18 suka nuna adawa da shi, sannan kuma kuri’u hudu aka bayyana ba su da inganci. An fara muhawara kan gyaran fuska ne kwanaki kadan a babban birnin kasar, Yaoundé.
Jagoran ‘yan adawa Maurice Kamto ya yi Allah wadai da matakin, yana mai bayyana shi a matsayin wani yunkuri na hada karfi da karfe, a wani jawabi da ya yi ranar Juma’a Da ta gabata.
A karkashin sabon tanadin, mataimakin shugaban kasar zai fara aiki kai tsaye a yayin da shugaban ya mutu, ko murabus, ko kuma rashin iya aiki, ba tare da bukatar sake gudanar da zabe ba. Wannan sauyin dai ya zo ne a daidai lokacin da ake duban shugaba Paul Biya, wanda a shekaru 93, ya sake samun wani wa’adi a zaben da aka yi ta cece-kuce a watan Oktoban da ya gabata.
Magoya bayan wannan gyare-gyaren suna jayayya cewa gabatar da mataimakin shugaban kasa zai karfafa zaman lafiyar hukumomi da kuma bada tabbacin ci gaba da shugabanci. Sai dai masu suka sun yi gargadin cewa zai iya gurgunta tsarin dimokuradiyya ta hanyar kawar da bukatar masu kada kuri’a na zaben magaji.
LABARAN AFRICA/A’isha. Yahaya, Lagos