Hukumomin kasar Sin da kamfanonin jiragen sama sun taimaka wa Sinawa sama da 10,000 da suka dawo daga Gabas ta Tsakiya.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce a ranar Talata da ta gabata, bayan yakin da aka yi a yankin ya tilasta rufe sararin samaniya da kuma dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana cewa, sama da Sinawa 10,000 ne suka dawo cikin koshin lafiya daga kasashen da suka hada da Masarautar Hadaddiyar Daular Larabawa, da Oman da kuma Saudiyya.
Guo ya ce, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama sun jagoranci kamfanonin jiragen sama na cikin gida da su kara karfin maido da ‘yan kasar Sin da suka makale a Gabas ta Tsakiya.
KU KARANTA KUMA: Kasar Sin ta jaddada kudirinta na karfafa mata a Najeriya& # 8217;
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce, an kwashe sama da ‘yan kasar Sin 3,000 daga Iran.
Yakin Gabas ta Tsakiya, wanda ya barke bayan da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hare-hare kan Iran a ranar 28 ga watan Fabrairu, ya kai ga soke tashin jiragen a yankin.
Manyan kamfanonin jiragen sama na kasar Sin, ciki har da Air China da kamfanonin jiragen sama na Kudancin China sun dawo da zirga-zirga a farkon wannan watan tsakanin wasu biranen kasar Sin da cibiyoyin Gulf kamar Riyadh da Dubai.
Kasar Sin ta yi Allah wadai da harin da Amurka da Isra’ila suka kai, inda ta yi kira da a tsagaita bude wuta, kana ta aike da jakada zuwa Gabas ta Tsakiya domin shiga tsakani.
Reuters/A’isha. Yahaya, Lagos