A baya-bayan nan ne kotun shari’a ta ECOWAS ta kira wani taron kasashen biyu a birnin Conakry na kasar Guinea, domin tantance matsayin aiwatar da hukuncin da ta yanke a Jamhuriyar Guinea.
Taron ya tattara hukumomin ƙasa da manyan masu ruwa da tsaki don ƙarfafa hanyoyin aiwatarwa, magance ƙalubale, da samar da dabaru masu amfani don haɓaka bin hukunce-hukuncen Kotuna.

Haɗin gwiwar bangarorin biyu wani bangare ne na ayyukan bikin cika shekaru 50 da kafa kungiyar ECOWAS.
Tawagar kotun karkashin jagorancin shugaban kotun Ricardo Cláudio Monteiro Gonçalves ta kuma gudanar da irin wannan tarurruka a kasashen Saliyo da Najeriya.
