Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar Iraqi Ta Tsayar Da Ranar 11 Ga Watan Afrilu Domin Zabe Shugaban Kasa

15

Majalisar dokokin Iraqi ta tsayar da ranar 11 ga watan Afrilu Mai Zuwa domin gudanar da zaben sabon shugaban kasa, a daidai lokacin da ake ci gaba da kokarin warware takaddamar siyasa da aka dade ana yi.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, fadar shugaban kasar ta ce an amince da ranar ne bayan da aka fadada taron da shugabannin kungiyoyin ‘yan majalisu domin kammala muhimman ayyukan majalisa da kuma kammala zabar kwamitoci masu zaman kansu.

Taron ya jaddada bukatar cika sharuddan da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada na zaben shugaban kasa da kuma kawo karshen takun sakar siyasa.

KU KARANTA KUMA: WHO Ta Saki Tallafin Gaggawa $2m ga Lebanon, Iraq, Syria

Sanarwar ta ce “Fadar shugaban kasa ta yi kira ga shugabannin kungiyoyin siyasa da su kiyaye nauyin da ya rataya a wuyansu na kammala ayyukan kundin tsarin mulkin kasar da kuma kafa gwamnatin da za ta iya tinkarar kalubalen da ake fuskanta a yanzu.”

Iraki ta gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a watan Nuwamban shekarar 2025. A karkashin kundin tsarin mulkin kasar, dole ne majalisar ta zabi shugaban kasa da kashi biyu bisa uku a cikin kwanaki 30 na zamanta na farko.

Wannan dai wani mataki ne na wajibi da ke gabanin gabatar da firaminista a hukumance daga babbar kungiyar majalisar dokoki domin kafa sabuwar majalisar ministoci mai cikakken ikon zartarwa.

Sai dai tsarin ya fuskanci tsaiko a lokuta da dama saboda rashin samun daidaito tsakanin manyan kungiyoyin siyasa, lamarin da ya bar kasar da gwamnatin rikon kwarya mai iyaka ta shari’a.

Yunkurin gaggauta kada kuri’a a halin yanzu na zuwa ne a daidai lokacin da Irakin ke fuskantar matsin lamba na daidaita yanayin siyasarta a cikin yanayi maras dadi a yankin.

A karkashin tsarin raba madafun iko na Iraki, an kebe kujerar shugaban kasa ga Kurdawa, shugaban majalisar dokoki ga musulmi ‘yan Sunni, da kuma firaminista ga musulmi ‘yan Shi’a.

 

 

NAN/A’isha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.