Take a fresh look at your lifestyle.

Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Yi Allah-Wadai Da Harin Jos

21

Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Mista Benjamin Kalu ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan harin da aka kai kan mazauna Angwan Rukuba da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato a yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya.

Harin wanda rahotanni suka ce ya faru ne a daren Lahadi ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ya jefa al’ummar cikin alhini.

Mista Kalu a cikin sakon ta’aziyyar ya bayyana matukar alhininsa kan wannan mummunan lamari, inda ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma gwamnatin jihar Filato, tare da addu’ar samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

Ya bayyana harin a matsayin rashin hankali da rashin yarda yana mai jaddada cewa dole ne a kiyaye tsarkin rayuwar dan Adam a kowane lokaci.

Mataimakin Shugaban Majalisar ya tabbatar wa mazauna yankin cewa hukumomin tsaro zasu dage wajen zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Ya yi kira da a kwantar da hankula a tsakanin mazauna yankin yana mai kira gare su “da su bada hadin kai da hukumomin tsaro ta hanyar samar da bayanai masu amfani da za su taimaka wajen gudanar da bincike.”

Mataimakin shugaban majalisar ya kara jaddada bukatar karfafa matakan tsaro a tsakanin al’ummomin da ke fama da rauni da kuma sabunta alkawari daga masu ruwa da tsaki domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar Filato da ma fadin kasar nan.

 

Comments are closed.