Take a fresh look at your lifestyle.

Mozambik Ta Ba Da Umarnin Kwashe Jama’a Saboda Barazanar Ambaliyar Ruwa

68

Kasar Mozambik ta ba da umarnin kwashe mazauna yankunan da ke karkashin kasa a cikin lardunan Inhambane, Gaza da Sofala, biyo bayan gargadin yiwuwar bullar ambaliyar ruwa a karo na biyu.

Shugabar Cibiyar Kula da Hatsari da Rage Hatsarin Bala’i (INGD), Luísa Meque ta bukaci al’ummomin da abin ya shafa da su kasance cikin taka-tsan-tsan tare da ƙaura zuwa wurare masu aminci don guje wa asarar rayuka da dukiyoyi.

Ta bayyana cewa “Hukumomi sun gano wuraren da aka kebe don karbar mutanen da suka rasa matsugunan su idan bukatar haka ta taso don kunna cibiyoyin matsugunin gaggawa.”

Ƙungiyoyin fasaha suna cikin ƙasa lardunan da abin ya shafa don sa ido kan yanayi da ƙarfafa matakan kariya.

Wannan kiran dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Mozambique ke ci gaba da kokawa da daya daga cikin lokutan damina mafi muni a cikin ‘yan shekarun nan.

Tun daga watan Oktoba, ambaliyar ruwa da guguwa sun kashe kusan mutane 280 tare da shafar kusan 900,000, a cewar alkaluman INGD.

Sama da gidaje 15,000 ne suka lalace yayin da daruruwan makarantu da cibiyoyin lafiya da wuraren ibada suka lalace.

Ambaliyar ruwa ta kashe akalla mutane 43 a watan Janairu yayin da guguwar Gezani da ta afkawa birnin Inhambane a tsakiyar watan Fabrairu, ta yi sanadin mutuwar wasu mutane hudu tare da raba dubbai da muhallansu.

Har ila yau, bala’in ya lalata noma, inda sama da hekta 267,000 na gonaki suka yi hasarar kuma an kashe fiye da dabbobi fiye da rabin miliyan.

Daminar ta Mozambique ta kan kai har zuwa watan Afrilu, inda ake fargabar cewa karin guguwa na iya dagula matsalar jin kai.

 

AP/A’isha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.