Gwamna Abba Yusuf ya yaba da komawar tsohon Gwamna kuma Sanata Ibrahim Shekarau zuwa jam’iyyar APC daga jam’iyyar PDP.
Gwamna Yusuf ya bayyana matakin a matsayin wani gagarumin cigaba da ke karawa jam’iyyar karfi a siyasar jihar Kano.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Mustapha Muhammad ya fitar, Gwamna Yusuf ya ce ana kan shirye-shirye tare da hadin gwiwar sakatariyar jam’iyyar ta kasa, domin kayyade ranar da Shekarau zai karbi bakoncin jam’iyyar APC.
Shekarau ya bayyana ficewar sa ga magoya bayan sa bayan tuntubar juna da kuma ziyarar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Nantawe Yilwatda ya kai gidansa na Kano.
Karanta Haka: Shugaban Jam’iyyar APC Yilwatda Ya Ziyarci Shekarau, Ya Kaishi APC
Yayin da yake maraba da Shekarau zuwa APC, Gwamna Yusuf ya jaddada cewa jam’iyyar na ci gaba da samun tagomashi a fadin jihar, tare da kara samun goyon baya da kawancen da ke kara karfafa matsayinta na kan gaba a siyasance a Kano.
A cewar gwamnan, jam’iyyar APC ta shirya tsaf domin gudanar da zabuka a nan gaba, kuma tana da yakinin samun nasara a dukkan mukaman da aka zaba, yana mai alakanta wannan kyakkyawan fata ga samun hadin kai da kuma kididdige tsarin siyasa a tsakanin ta.
Gwamna Yusuf ya kara tabbatar wa ‘ya’yan jam’iyyar kan kudirin gwamnatinsa na kara zurfafa hadin kan cikin gida tare da kara fadada jam’iyyar a cikinta.
Ya bukaci masu biyayya da magoya bayansa da su jajirce tare da kara zage damtse a yayin da jam’iyyar APC ke shirin tunkarar fafatawa a siyasance.
A’isha. Yahaya, Lagos