Dakarun Sojin Gidan sarautar Ingila sun karrama Shugaba Tinubu da Uwargidan shi Remi Tinubu a bikin karbar ziyarar shugaban Najeriya zuwa Kasar Burtaniya.
Tun farko an gudanar da liyafar tarbar shugaban Najeriya a dakin Taro na Windsor Castle tare da tattaunawar Diplomasiya kai tsaye.
Kafin taron Yarima da Gimbiyar Wales Pl William da Catherine sun tarbi Shugaba Tinubu da Uwargidan shi a Hutel din Faitmont kafi a kaisu babban dakin taro na Windsor inda suka gana da Sarki Charles na III.

Daga cikin shirin bangarorin biyu sun yi musayar kyautuka daga bisani aka gabatr da baje kolin kayayyakin tarihin Najeriya da aka ajiye su a fadar Sarki.
Hakazalika ziyarar ta kuma karrama tawagar najeriya a dakin taron daga bisani Shugaba Tinubu da Sarki Charles na III zasu gabatr da bayanai ga shugabannin duniya da manyan wakilai da suka halarci taron.
Kafin a kamala ziyarar ana sa ran Shugaba da Uwargidan shi zasu ziyarci kabarin Sarauniya Elizabeth na II dake St George’s Chapel.

Ana sa ran Tawagar zata gana da shugabannin Addinai da kungiyoyi domin yada kyawawan manufofi da yada kyawawan akidun zamantakewa da juna.
Kamar yadda shirin ya kunsa Shugaba Tinubu zai tattauna da Keir Starmer a ranar Alhamis tare da tattaunawa da al’ummar Najeriya mazauna kasashen waje tun farko ma sai da Sarki Charles na III ya shirya wa ‘yan Najeriya mazauna Burtaniya a fadar St James.

Tattaunawar zata bun kasa dankon alaka tsakanin Najeriya da Burtaniya inda za’a maida hankali akan harkokin tsaro da Kasuwanci da shugabanci musamman ci gaban siyasa.