Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Dawo Bayan Ziyarar Kasar Turkiyya

142

Shugaba Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan kammala ziyarar aiki a Jamhuriyar Turkiyya cikin nasara, inda ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da karfe 8:55 na dare.

Da ya isa Abuja, shugaban ya samu karba daga ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike; Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun; da kuma karamin ministan tsaro, Bello Matawalle.

Komawar Shugaba Tinubu ta biyo bayan wasu manyan ayyuka da aka yi a Ankara wanda ya kara tabbatar da sabunta huldar diflomasiyya da Najeriya.

A yayin ziyarar, shugaban na Najeriya ya tattauna da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, tare da ganawa da manyan jami’an gwamnati da shugabannin masana’antun tsaro.

Ziyarar da aka yi a kasar ta samu sakamako mai ma’ana, ciki har da yadda Turkiyya ta jaddada kudirinta na zurfafa hadin gwiwa da Najeriya a fannin tsaro, horar da sojoji da musayar bayanan sirri, da kuma goyon bayan yakin da Najeriya ke ci gaba da yi da ‘yan tada kayar baya.

Kazalika, kasashen biyu sun jaddada aniyarsu ta cimma burin cinikin dalar Amurka biliyan 5, wanda ke nuni da fadada huldar tattalin arziki.

A yayin ganawarsa da shugaba Erdogan, shugaba Tinubu, ya bayyana godiya ga gwamnatin Turkiyya bisa yadda ta bude hadin gwiwa, inda ya bayyana cewa, an tattauna batutuwan da suka shafi yaki da ta’addanci, da bunkasar tattalin arziki, da kokarin hadin gwiwa wajen fatattakar ‘yan ta’adda da ke barazana ga zaman lafiya a yankin.

 

Aisha. Yahaya, Lagos

 

Comments are closed.