Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jajanta wa ‘yan kasuwa da mazauna jihar Kano biyo bayan wata mummunar gobara da ta barke a kasuwar Singer, inda ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan abubuwan da ke faruwa a cibiyar kasuwanci.
Gobarar da ta tashi da yammacin ranar Asabar da ta gabata, ta yi barna sosai a kasuwar kayayyakin abinci, inda ta lalata kayayyaki da kayayyakin more rayuwa.
Shugaba Tinubu, wanda tun da farko ya tuntubi Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf don samun rahoton halin da ake ciki, ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tausayi da matukar damuwa.
Shugaban ya nuna fargabar cewa gobarar ta baya-bayan nan ta afku ne kasa da makonni biyu bayan wata gobara da ta tashi a kasuwar daya barnatar da shaguna da kadarori da dama.
Shugaba Tinubu ya kuma ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan musabbabin tashin gobarar da ke faruwa a kasuwar, inda ya ce irin wannan lamari ya sha jefa ‘yan kasuwa cikin kunci da kuma lalata rayuwa.
Ya bukaci hukumomin da abin ya shafa da su karfafa matakan tsaro da tsarin rigakafin gobara a manyan kasuwanni a fadin kasar don kaucewa bala’i a nan gaba.
Aisha. Yahaya, Lagos