Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya mika sakon taya murna ga al’ummar Musulmi a Najeriya da ma duniya baki daya, dangane da bukukuwan karamar Sallah da aka yi, na karshen watan Ramadan.
A cikin sakon fatan alheri da kakakin shugaban kasa, Mista Bayo Onanuga ya fitar a ranar Alhamis da ya gabata , shugaba Tinubu ya yi kira ga musulmi da su sabunta alkawarinsu ga kasa da kuma bil’adama.
Ya bukace su da su kiyaye dabi’u masu dorewa na takawa, tausayawa, hadin kai, da jin kai da ake rayawa a lokacin azumi.
Shugaban ya jaddada bukatar ‘yan Najeriya su ‘dauwama da kyawawan dabi’u kamar rashin son kai, dagewa, kyautatawa, da jin kai fiye da watan mai alfarma.
“Muna da abubuwa da yawa da za mu ciro daga darasin darussa na Ramadan, musamman a irin wannan lokaci, dole ne mu ci gaba da kiyaye kyawawan dabi’u na takawa, rashin son kai, dagewa, kyautatawa da jin kai bayan wannan lokaci,” inji shi.
Shugaba Tinubu ya kuma kara karfafa gwiwar musulmi da su kara kaimi ga masu karamin karfi, ba tare da la’akari da addini ba, a matsayin nuna hadin kai da dan Adam.
Ya kuma bukaci malaman addini da su yi amfani da bikin Eid-el-Fitr wajen gudanar da addu’o’in samun dawwamammen zaman lafiya, kwanciyar hankali da wadata a kasar nan.
A’isha. Yahaya, Lagos