Rundunar hadin gwiwa ta (Arewa maso Gabas) Operation HADIN KAI ta kara zage damtse wajen dakile ayyukan ta’addanci da hanyoyin samar da kudade a yankin.
A wani jerin ayyuka na hadin guiwa, sojojin sun kwato wasu makudan kudade tare da kama Naira miliyan 37 da ake zargin suna da alaka da tallafawa ‘yan ta’adda.
Ayyukan, wanda aka gudanar a ranar 16 ga Fabrairu, 2026, sun hada da wani harin kwantan bauna da dare a kan hanyar da ‘yan ta’adda suka sani na tsallakawa da kuma tsagaita wuta da wata mota da ake zargi a mashigin Chabbal.

Kudade da kayyakin da aka kwato a cikin wata sanarwa da Laftanal Kanal Sani Uba, kakakin rundunar ya fitar, ana kyautata zaton cewa an yi amfani da su ne domin ayyukan ta’addanci, kuma ana sa ran kama su zai kawo cikas ga ci gaban ‘yan ta’addan.
Rundunar sojin ta yabawa sojojin da hadin gwiwar jami’an tsaro bisa yadda suke taka-tsantsan da sanin makamar aiki.
Rundunar ‘Operation HADIN KAI’ ta dukufa wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Arewa maso Gabas.
Aisha. Yahaya, Lagos