Take a fresh look at your lifestyle.

Uganda ta musanta samun karuwar cutar Ebola da ke da alaka da gasar gudun Fanfalaki

Aisha Yahaya

1 383

Ma’aikatar lafiya ta Uganda ta musanta ikirarin cewa wani taron gudu da aka gudanar a karshen makon da ya gabata a Kampala babban birnin kasar, wani lamari ne mai yaduwa da cutar Ebola.

 

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar ta ce babu wani mahaluki a gasar gudun marathon da ya gabatar da wata alama ta kwayar cutar mai saurin kisa. Ya kara da cewa babu wani mai dauke da cutar Ebola da aka yi rajista a babban birnin kasar fiye da wadanda aka kebe.

 

A halin da ake ciki, kasar na fama da bullar cutar Ebola da ya zuwa yanzu ta kashe mutane sama da 50. An rufe makarantu tare da sanya dokar hana fita a wasu gundumomi biyu da ake tunanin sune farkon barkewar cutar. Hukumomin kasar sun ce an yi kokarin hana fitar da cutar zuwa wasu sassan kasar.

One response to “Uganda ta musanta samun karuwar cutar Ebola da ke da alaka da gasar gudun Fanfalaki”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *