Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya koma Abuja bayan ya wakilci shugaban kasa Bola Tinubu a wajen taro na 39 na shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Afrika (AU) da kuma babban taron kungiyar AU karo na 30 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
Taron AU na bana, wanda aka gudanar tsakanin ranakun 14 da 15 ga Fabrairu, 2026, mai taken, “Tabbatar da Samar da Ruwa mai dorewa da Tsafta don Cimma Manufofin Ajandar 2063,” ya mai da hankali kan ci gaba da alkawurran da kasashen nahiyar suka dauka wajen kula da ruwa mai dorewa, da inganta tsarin tsafta.
Taron ya kuma duba manyan buri na ci gaban da aka kulla a cikin ajandar AU ta 2063.

Baya ga tarukan shugabannin kasashen, mataimakin shugaban kasar ya kuma halarci manyan tarurrukan da suka shafi bangarorin biyu, ya kuma gudanar da huldar kasuwanci da shugabannin siyasa da na kasuwanci da nufin karfafa huldar diflomasiyya, tattalin arziki, da manyan tsare-tsare na Najeriya a fadin nahiyar.
Ya samu amincewar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, wanda ya bukaci Najeriya da ta jagoranci yunkurin Afirka na sake fasalin tsarin duniya, yana mai bayyana kasar a matsayin wacce ta ke da matsayi na musamman don jagorantar nahiyar zuwa matsayi mai karfin gaske.
A madadin shugaba Tinubu da Najeriya, mataimakin shugaban kasar ya kuma yi kira da a sauya nahiyar Afirka wajen tabbatar da tsaron da lafiya a nahiyar Afirka da nufin kawar da nahiyar daga dogaro da tallafin kasashen waje zuwa tsarin kiwon lafiya na gida mai dogaro da kai.
Aisha. Yahaya, Lagos