Yayin da Jihar sokoto ke cigaba da yaki da matsalar karancin ruwa Hon. Faruk Sarkin Fada ya raba wa al’umma da dama daga cikin tankunan ruwa da bai gaza 50 ba.
Da yake jawabi ga manema labarai a gidansa Hon. Sarkin Fada ya ce an kaddamar da shirin na kashin kansa ne a wani bangare na taimakon agajin da ya ke yi domin rage radadi a tsakanin mutanen da ke cikin mawuyacin hali a Jihar.
Ya kara da cewa matsalar karancin ruwan da ake fama da ita na da nasaba da rashin samar da wutar lantarki da ya shafi ayyukan hukumar samar da ruwan sha ta jihar wanda hakan ya sa gidaje da dama ke kokawa wajen samun ruwa mai tsafta.
“Birnin Sokoto babban birni ne mai yawan jama’a amma duk da haka ba mu da isasshen ruwan sha saboda matsalolin da ake fama da su a hukumar ruwa na kasa ba Za iya zama ina kallon yadda jama’a mu ke shan wahala a matsayina na Dan asalin Sakkwato ba ina ganin kowane mazaunin gida Dan uwa ne ko kanwa.
“Ya zuwa yanzu mun kai kusan tankokin ruwa 50 ga al’ummomi daban-daban tare da shirye-shiryen gwargwadon iko.
“Yankunan da suka amfana sun hada da Kofar rini Kofar Marke da Kanwuri Madunka da kofar taramniya da kofar Atiku da sauransu” in ji shi.
Ya ce ya mayar da hankali kan wadannan yankuna ne saboda yawan jama’a da ke fama da matsalar lafiya idan aka ci gaba da fuskantar karancin ruwa.
Ya kara da cewa lamarin ya zama batu mai dadewa wanda kokarin gwamnati bai samar da dawwamammen mafita ba don samun kwanciyar hankali.
Ya bukaci gwamnatin Jihar da ta ba da fifiko ga tsarin samar da ruwa mai dorewa inda ya ba da shawarar manyan ayyukan rijiyoyin burtsatse da zuba jari a manyan injina don samar da wutar lantarkin da ake da su.
“Ruwa ita ce rayuwa. Idan ba tare da shi ba ba za ku iya cimma komai ba. Dole ne gwamnati ta kasance da niyya da Kuma dabarun magance wannan rikici,” in ji shi.
Sarkin Fada ya bayyana cewa tuni ya nutsar da rijiyoyin burtsatse guda uku a Sakkwato kuma yana shirin gina wasu wurare a Sakkwato ta Arewa da ta Kudu kowanne wanda zai iya tanadin ruwa har lita dubu ashirin da biyar (25000) domin hidima ga gidaje da ke kewaye.
Bayan ayyukan ruwa ya ce ana shirin kaddamar da wani shiri da nufin karfafa tattalin arzikin mata da matasa a Jihar.
“Wadannan sun haɗa da shirin horar da mata da aka mayar da hankali kan samar da abinci a cikin gida da kuma tattara kayan miya da kayan ciye-ciye wani shiri da ke da irinsa na farko a Najeriya.
“Ina so in fara da mata 100, 50 daga Sokoto arewa da 50 daga Sokoto ta kudu kuma a karshe za su kai dari 200.
Hakan zai taimaka musu wajen samun kwarewa da samar da kudin shiga da kuma inganta tattalin arziki a Sokoto ” in ji Jigon PDP.
Aisha.Yahaya, Lagos