Take a fresh look at your lifestyle.

Firaministan Libiya Ya Bayyana Cewa Ana Ci Gaba Da Wargaza ‘Yan Bindiga

37

Firayim Ministan Libya Abdulhamid Al-Dbeibah ya fada a ranar Asabar da ta gabata cewa kawar da mayakan sa kai wani aiki ne da ke ci gaba da gudana a matsayin tsagaita bude wuta bayan kazamin fadan da ya barke a wannan makon.

Dbeibah wanda shi ne shugaban kasar da kasashen duniya suka amince da shi a yammacin kasar wanda ke da hedkwata a birnin Tripoli ya ce “Ba za mu kyale duk wanda ya ci gaba da cin hanci da karbar rashawa ba. Burinmu shi ne samar da kasar Libiya da ba ta da ‘yan bindiga da cin hanci da rashawa.”

A ranar Talata da gabata ne ya ba da umarnin wargaza kungiyoyin da ke dauke da makamai Tripoli ta fuskanci kazamin fada mafi muni cikin shekaru tsakanin kungiyoyin biyu masu dauke da makamai. Rikicin ya yi sanadiyar mutuwar akalla fararen hula takwas a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Gwamnati ta sanar da tsagaita bude wuta a ranar Laraba. Hakan ya biyo bayan kashe babban hafsan mayakan sa kai Abdulghani Kikli wanda aka fi sani da Ghaniwa da aka yi a ranar litinin da ta wuce da kuma kashin kungiyoyin da ke da alaka da Dbeibah suka yi da kungiyarsa ta Stabilization Support Apparatus.

SSA tana karkashin Majalisar Shugaban kasa da ta hau karagar mulki a shekarar 2021 tare da Gwamnatin hadin kan kasa ta Dbeibah ta hanyar da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya. An kafa ta ne a unguwar Abu Salim mai yawan jama’a.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta GNU a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce an gano gawarwaki tara (9) da suka ruguje a cikin wani firjin ajiye gawa a asibitin Al-Khadra da ke Abu Salim. Ta ce SSA ba ta kai rahoto ga hukumomi ba.

Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.