Take a fresh look at your lifestyle.

NSF: NSC Ta Hana ‘Yan Wasa 6 Shiga Gasar Wassanin Motsa Jiki.

40

Hukumar kula da wasannin motsa jiki ta kasa (NSC) ta ce ta haramta wa ‘yan wasa shida shiga gasar wasannin motsa jiki ta kasa (NSF) na 22 da ake yi wa lakabi da Gateway Games.

Darakta Janar na NSC (DG) Bukola Olopade ya bayyana wa manema labarai a ranar Talata din da ta gabata a Abeokuta cewa rashin cancantar na da nasaba da batun hana kara kuzari.

Ya ci gaba da cewa ’yan wasa masu rijista da ke da matsalar hana kara kuzari ba za su iya yin gasa don samun lambobin yabo a wasannin Gateway da ke gudana ba.

Matakin na zuwa ne bayan wani babban taro na hadin gwiwa na babban kwamitin shirya gasar (MOC) da (LOC) na wasannin.

Hukumar ta sanar da cewa hakan ya yi dai-dai da mafi kyawu a duniya da kuma ka’idar hukumar yaki da shan kwayoyi ta duniya WADA.

Olopade ya bukaci daukan Jihohin kasar da su lura da hakan tare da jaddada kudirin Hukumar na tabbatar da cewa kowane dan wasa ya yi tsaft.

NSF: Jihar Ogun Ta Yi Alkawarin Kyautar N2.5m Ga Masu Yakin Zinare

Batun hana amfani da kwayoyi masu kara kuzari wani muhimmin aiki ne na hukumar don a tabbatar da cewa Najeriya ba ta da matsalar muggan kwayoyi a wasannin gida da waje.

“Muna farin ciki a yanzu cewa a karshe dokar hana kara kuzari ta kasa ta amince da dokar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kuma dole ne a ga tasirin irin wannan gagarumin aiki cikin gaggawa a wasanninmu da aka fara da bikin wasanni na kasa,” in ji shi.

‘Yan wasan da abin ya shafa sun hada da Marcus Okon mai wakiltar Jihar Akwa Ibom a Para Athletics da Ayabeke Opeyemi mai wakiltar Jihar Bayelsa a Gymnastics da Shukurat Kareem mai wakiltar Jihar Legas a damben bugun daga kai sai kuma Omole Dolapo Joshua mai wakiltar Jihar Bayelsa a wasan bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Sauran sun hada da Ogunsemilore Cynthia mai wakiltar Jihar Bayelsa a wasan dambe da Animashaun Sofia mai wakiltar Jihar Legas a Para powerlifting.

 

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.