Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Gombe Ya Sanya Hannu Kan Dokar Samar Da Wutar Lantarki A 2025

36

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya sanya hannu kan dokar samar da wutar lantarki ta jihar Gombe 2025. Dokar wacce Majalisar Dokokin Jihar Gombe ta fara aiwatarwa a ranar 29 ga Afrilu, 2025, ta samu amincewar Gwamna a ranar 5 ga Mayu 2025.

Sabuwar dokar ta baiwa gwamnatin Jihar damar kula da duk wani nau’i na darajar wutar lantarki  tun daga samarwa zuwa amfani tare da karfafa gwiwar kamfanoni masu zaman kansu da hadin gwiwar gwamnati .

Hakanan yana inganta fadada wutar lantarki ta hanyar samfura iri-iri game da Grid  tsarin da ba a sabunta su ba.

Matakin ya kuma yi daidai da tanadin dokar samar da wutar lantarki ta gwamnatin tarayya na shekarar 2023 da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa hannu  wadda ta umarci kananan hukumomi su kafa nasu tsarin shari’a na sarrafa wutar lantarki a yankunansu.

Dokar samar da wutar lantarki ta Jihar Gombe a 2025 ta ba da ka’ida ga Jihar ta yi amfani da ikonta na tsarin mulki kan al’amuran wutar lantarki da ke faruwa a cikin iyakokinta.

A hukumance ta kafa kasuwar wutar lantarki ta Jihar Gombe da hukumar kula da wutar lantarki ta Jihar Gombe (GSERC).

Wadannan cibiyoyi ne za su dauki nauyin tsara yadda ake samar da wutar lantarki  watsawa  rarrabawa da kuma yadda ake gudanar da ayyukan wutar lantarki a fadin Jihar.

Jihar Gombe tana da dabarun da za ta amfana da wannan tsarin doka.

A matsayinta na daya daga cikin Jihohin da ke samar da wutar lantarki a Najeriya  ta dauki nauyin tashar samar da wutar lantarki ta Dadinkowa wanda ke ba da gudunmowar kusan megawatt 40 ga wutar lantarki ta kasa.

Baya ga samar da wutar lantarki  Jihar na da dumbin ma’adanar da man fetur da iskar gas  da albarkatun da ke da karfin bunkasa masana’antu da isar da ingantaccen makamashi ga gidaje da kasuwanin.

A nasa jawabin kwamishinan makamashi da albarkatun ma’adinai  Malam Sanusi Ahmed Pindiga ya bayyana cewa ta hanyar kafa dokar samar da wutar lantarki ta kasa Jihar Gombe tana cika ka’idojin gwamnatin tarayya da kuma shimfida hanyar dogaro da kai da samun ci gaba mai dorewa da kuma habaka tattalin arziki.

Dokar samar da wutar lantarki ta Jihar Gombe 2025 tana wakiltar wani babban ci gaba a burin Gwamna Inuwa Yahaya na sake fasalin makamashin Jihar da karfafawa al’ummomin yankinn da kuma bunkasa masana’antu na dogon lokaci,” in ji shi.

Wannan ci gaban na majalisar ya zo ne jim kadan bayan da gwamnatin Jihar Gombe ta amince da kashe Naira biliyan 5.5 don kammala aikin dajin masana’antu na Muhammadu Buhari da ke Dadinkowa  aikin na biliyoyin nairori wanda tuni ya jawo dimbin masu zuba jari da masana’antu a Jihar.

Daga cikin manyan masu saka hannun jari akwai Three Ace Technologies kamfanin samar da wutar lantarki da ke shirin samar da sama da megawatts 150 na makamashin hasken rana don hidima ga masana’antu na cikin gida da sauran yankuna.

Aisha. Yahaya, Lagos

Comments are closed.