Majalisar ECOWAS ta amince da wani tsarin da aka yi wa kwaskwarima da nufin inganta ado da mutunta juna a tsakanin mambobinta.
Sabbin dokokin sun haramtawa membobin yin kalaman batanci ko rashin mutuntawa kan ‘yan majalisar dokoki da shugabannin kasashe a yankin yammacin Afirka.
Ana kallon wannan matakin a matsayin wani bangare na kokarin karfafa hadin kai da kiyaye ka’idojin diflomasiyya a cikin kungiyar kasashen yankin.
‘Yan majalisar yankin sun amince da dokar da aka yi wa kwaskwarima a zaman farko na majalisar da aka yi ranar Alhamis din da ta gabata a Abuja.
Dan majalisa Billay Tunkara mataimakin kakakin majalisa na hudu kuma shugaban kwamitin Ad-Hoc na rahoton wanda ya gabatar da takardar ya bayyana cewa gyare-gyaren da aka yi da nufin kara tabbatar da gaskiya da rikon amana da gudanar da mulki mai inganci a majalisar.
Dokokin da aka yi wa kwaskwarima sun kuma nuna cewa mambobin da suka gaza kashi daya bisa uku na zaman majalisar ba tare da hujja ba za a hukunta su sannan kuma za a dakatar da alawus din su na zama.
Canje-canjen ya kuma tanadi daidaiton jinsi da harshe a cikin nadin kwamitoci da tsara ka’idojin tufafi don nuna martabar majalisar da kuma adadin mambobi 50+ da za su fara zama.
Sabbin Dokokin sun kuma tanadi cewa domin a kiyaye nuna son kai Shugaban Majalisar na iya shiga muhawara ne kawai bayan ya bar kujerarsa na wani dan lokaci zuwa Mataimakin Shugaban Majalisar.
“Ana sa ran amincewa da ka’idojin da aka yi wa kwaskwarima zai inganta halarta da’a da kuma ingancin muhawara a cikin ECOWAS,” in ji takardar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa zaman majalisar dokokin yankin na 2025 wanda aka fara ranar Talata da ta gabata zai kare ne a ranar 31 ga watan Mayu.
Taron ya kuma gabatar da jerin ayyuka da aka tsara don cika shekaru 25 na majalisar daga baya a watan Nuwamba.
Abubuwan da suka faru na nufin haɓaka haɗin kai da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe membobin ECOWAS
NAN/Aisha. Yahaya, Lagos