Take a fresh look at your lifestyle.

Kotun Kenya Ta Yanke Wa Mutum Biyu Hukuncin Kisa A Shekarar 2019.

34

A ranar Alhamis din da ta gabata ne wata kotu a kasar Kenya ta samu wasu mutane biyu da laifin taimakawa harin ta’addancin da aka kai a wani otel da ofishi a birnin Nairobi a shekarar 2019 wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 21. Alkalin kotun ya ce mayakan da ke da alaka da al-Qaeda ne suka kai harin.

A watan Janairun 2019 wasu ‘yan bindiga sun bindige kan hanyarsu ta zuwa otal da ofishin Dusit na Nairobi inda suka kashe mutane 21 a wani kawanya da ya dauki sama da sa’o’i 12

A lokacin gwamnatin kasar ta ce ta kashe dukkan maharan wadanda ‘yan Somaliya ne da kuma ‘yan kungiyar al Shabaab wadda ta dauki alhakin kai harin.

Gwamnati ba ta bayyana adadin ‘yan bindigar da suka shiga cikin harin ba amma faifan CCTV da ke harabar ginin ya nuna maharan biyar.

Lauyoyin da ke wakiltar Bertrice Pompe dan kasar Birtaniya haifaffen tsibirin Chagos ne an ba su izinin wucin gadi a babbar kotun kasar da sanyin safiyar Alhamis.

Hukumomin kasar sun kama Hussein Mohammed Abdile da Mohamed Abdi Ali a karshen wannan shekarar saboda bayar da tallafin kayan aiki ga maharan.

A baya dai an yanke wa wanda ake zargi na uku Mire Abdullahi hukuncin daurin rai da rai bayan wata yarjejeniya da ta yi. Abdile da Ali sun musanta aikata laifin.

An dai zargi mutanen uku da bayar da tallafin kudi da kayan aiki ga ‘yan bindigar kuma ana tuhumar su da hannu wajen taimakawa da hada baki wajen aikata ta’addanci.

Masu gabatar da kara sun ce sun taimaka wa biyu daga cikin maharan samun takardun shaida na jabu wanda ya ba su damar tserewa daga sansanin ‘yan gudun hijira.

“Na sami wadanda ake tuhuma da laifi kuma a kan haka na yanke musu hukunci,” in ji mai shari’a Diana Mochache, ta kara da cewa za a yanke musu hukunci a wata mai zuwa.

Kenya dai na sha fuskantar hare-haren kungiyar Al Shabaab inda ta kashe mutane 67 a cibiyar kasuwanci ta Westgate a shekarar 2013 da kuma dalibai kusan 150 a jami’ar Garissa a shekarar 2015.

Kungiyar Al Shabaab da ta shafe shekaru goma tana neman hambarar da gwamnatin tsakiyar Somaliya mai rauni ta ce hare-harenta na ramuwar gayya ce ga Kenya da ta tura sojojinta domin yakar masu jihadi a yankin kahon Afrika.

 

 

Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos

 

 

 

Comments are closed.