Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama zai bar birnin Accra a ranar Lahadi 1 ga Maris, 2026, zuwa Arusha na kasar Tanzaniya, inda zai kasance babban bako na musamman a bikin bude shekarar shari’a ta 2026 na kotun Afrika mai kare hakkin bil’adama da jama’a a ranar Litinin mai Zuwa.
A cewar rahoton da kungiyar APO ta raba a madadin fadar shugaban kasar, Jamhuriyar Ghana, za a kuma yi amfani da bikin kaddamar da bikin cika shekaru 20 da kafa kotun.
A cewar rahoton, wannan ita ce gayyata ta farko ga shugaba mai ci na Jamhuriyar Ghana, don yin jawabi ga kotun AU, mai taken ‘Shekaru 20 na hidimar kare hakkin bil’adama da al’umma a Afirka.
“Yayin da yake Arusha, Shugaba Mahama zai tattauna da shugabar Tanzaniya, mai girma Samia Suluhu Hassan.
Rahoton ya kara da cewa “Mista Mahama zai bar Arusha bayan bude shirin a ranar Litinin, kuma yayin da yake tafiya, mataimakin shugaban kasar zai yi aiki a matsayin shugaban kasa kamar yadda doka ta 60 (8) ta tanadar.”
Aisha. Yahaya, Lagos