Take a fresh look at your lifestyle.

Macron Ya Ziyarci Vietnam, Yana Neman Hadin Kai Kkan Tsaro, Makamashi Da Ƙirƙire Ƙirkire

28

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya isa birnin Hanoi a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya fara rangadin mako guda a yankin Asiya da nufin kara dankon zumunci a fannin tsaro, makamashi, da sabbin fasahohi.

Wannan dai ita ce ziyarar farko da shugaban Faransa ya kai a Vietnam cikin kusan shekaru goma.

Macron wanda daga baya zai je Indonesia da Singapore, ya ce yana fatan kulla sabuwar huldar abokantaka a yayin da Faransa da Tarayyar Turai ke neman karfafa huldar kasuwanci a yankin Asiya a daidai lokacin da ake samun rashin tabbas kan manufofin kasuwancin Amurka karkashin Donald Trump.

Macron ya buga a kan X, “Na zo nan don ƙarfafa haɗin gwiwarmu a sassa masu mahimmanci: tsaro, kirkire-kirkire, canjin makamashi, da al’adu.”

Ana sa ran zai sanya Faransa da EU a matsayin zakara na ra’ayin bangarori daban-daban da kasuwanci na gaskiya, inda ya bambanta tsarinsu da abin da ya kira dabarun tilastawa ko farauta da kasashe kamar Amurka da China ke amfani da su.

Macron zai kammala ziyarar tasa ne a taron tattaunawa na Shangri-La a Singapore, babban taron tsaro na Asiya, inda zai bayyana kudurin Faransa na tabbatar da zaman lafiya a yankin da hadin gwiwar kasa da kasa.

Comments are closed.