โ๐ฌ๐ฎ๐ป๐๐ฎ๐ป๐ฑ๐ฎ ๐๐๐ป ๐ธ๐ฎ๐บ๐ฒ ๐บ๐ฎ๐๐ ๐ด๐ฎ๐ฟ๐ธ๐๐๐ฎ ๐ฑ๐ฎ ๐บ๐๐๐ฎ๐ป๐ฒ ๐๐ฎ๐บ๐ฎ ๐ฑ๐ฎ ๐ญ๐ฑ ๐ฎ ๐๐ฎ๐ป๐ผ
Yusuf Bala Nayaya,Kano>
Rundunar โyansandan jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya ta yi nasarar kame masu aikata miyagun laifuka sama da 25 da suka hada da masu garkuwa da mutane 16 da dillalin kayan maye.
A yammacin ranar Alhamis ne dai kwamishinan โyansandan Najeriya reshen jihar Kano Usaini Gumel ya bayyana gagarumar nasarar da rundunar โyansandan jihar ta yi na kame mau aikata miyagun laifukan.
A cewar Usaini Gumel a miyagun laifuka da ake aikatawa a jihar ta Kano an gano mummunar rawa da shan miyagun kwayoyi ke takawa don haka ne ma ya sanya dakarunsa suka fantsama a jihar don zakulo masu siyar da miyagun kwayoyin.
Cikin masu laifin da aka gabatar aka kuma basu dama su yi magana yayin taro manema labarai a shelkwatar โyansanda da ke Bompai sun hadar da mace mai kimanin shekaru 25 da ta yi garkuwa da โyar da ta haifa don neman kudin fansa Naira miliyan uku. Wannan mata dai Rahama Suleiman daga karamar hukumar Madobi ta bayyana cewa babu abin da mijin yayi mata ta shirya garkuwa da โyarsa. Bata dai samu kudinba an kuma yi nasarar kamata, sai dai da aka ji ta bakin mijinnata ya ce aikin shedan ne kuma tuni dama ya ma mayar da matartasa dakinta. Jamiโan โyansandan dai tuni suka tisa keyar matar da sauran masu laifukan don ci gaba da bincike.
Akwai kuma dila na tabar wiwi Ashiru Muhammad daga unguwar Kurnaย da aka kama da dauri dauri na wiwi sama da 600 da a cewar kwamishinan yansanda Gumel da yayi nasarar shiga da ita cikin alโumma da an kara samun yawaitar masu laifuka. Don ba da dadewa ba ne aka samu matashi da sanadin shan kayan maye ya kasha mahaifiyarsa a Kano.
Hakazalika rundunar tayi nasarar kama wata matar da ta sa aka kama dan kaninta inda suka nemi kudin fansa miliyan biyar an kumaย biya wanda ya karbi kudin ya arce a cewarta, rundunar dai na ci gaba da nemansa . Haka nan wasu gungun โyanfashi da makami da suka je fashin a karamar hukumar Tofaย a kokarin harbe wanda akayi garkuwa da shiย suka harbe abokin fashin nasu a cewar Idris Abdullahi jagoranย taasar.
Kwamishinaย Usaini Gumeldai yaceย muddin alโumma za su ci gaba da basu hadin kai da sannu za su tsince irin wadannan baragurbin mutane cikin alโummar jihar ta Kano.
Leave a Reply