Take a fresh look at your lifestyle.

An Kashe Sojojin Mali A Kwanton Bauna

0 166

Sojojin Mali 6 ne suka mutu sannan tara suka samu raunuka a farkon makon nan a wani harin kwantan bauna da aka kai a sansanin sojojin Mali kusa da Bamako a yammacin kasar, daga majiyoyin ‘yan sanda da kuma wani zababben jami’in yankin.

 

 

Majiyar ‘yan sandan ta ce an yi wa sojojin kwanton bauna ne a wannan yanki da ke kusa da garin Badala, kusa da Kita mai tazarar kilomita 130 daga babban birnin kasar, in ji majiyar ‘yan sandan ba tare da bayyana yanayin harin da kuma wadanda suka kai harin ba.

 

 

Wani dan siyasa a kasar ya tabbatar da mutuwar sojoji shida da raunata 9 ga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, wanda ya ce “‘yan ta’adda” ne suka kai harin, kalmar da ake amfani da ita a Mali wajen ayyana ‘yan jihadi.

 

 

Ba a yi ikirarin kai harin ba.

 

 

Martanin da sojojin suka bayar ya haifar da “mutuwar da dama” a cikin maharan, kamar yadda majiyar ‘yan sandan ta kara da cewa, ba tare da bayar da karin bayani ba.

 

 

Tun shekarar 2012 ne kasar ta Mali ke fama da matsalar yaduwar ‘yan ta’adda da kuma rikicin siyasa da tattalin arziki da kuma na bil adama.

 

Kanar-kanar da suka hau kan karagar mulki a shekara ta 2020 kuma aka yi juyin mulki karo na biyu a shekara ta 2021 sun rabu da tsohuwar kawancen Faransa da abokan huldarta, kuma sun koma ta fuskar soji da siyasa ga Rashawa.

 

 

A halin da ake ciki kuma, akalla sojojin Rasha biyu da wani farar hula guda sun mutu a daren jiya Talata, sakamakon fashewar gurneti a wata mashaya da ke tsakiyar kasar Mali, inda suke shan giya, in ji majiyoyin cikin gida.

 

 

A daren Talata, “an yi hadari a mashaya Tam-Tam a Segou. Wani malami dan kasar Rasha ya yi amfani da gurneti kuma an samu fashewar wani abu. An kashe ‘yan Rasha biyu. Akwai kuma wani farar hula da ya mutu,” in ji wani jami’in ‘yan sanda a birnin.

 

 

Wani zababben jami’in yankin ne ya tabbatar da hakan. Ya ce sojojin Mali biyu ma sun mutu.

 

 

“Wasu sojoji sun shigo mashaya. Sun yi odar giya. Suma wasu a aljihunsu. Mun ji hayaniya ga sojojin Mali da na Rasha. Akalla mutane uku ne suka mutu, ciki har da ‘yan kasar Rasha biyu. Wani farar hula ma ya mutu,” in ji wani shaida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *