Hukumomi a Hadaddiyar Daular Larabawa sun kama Asim Ghafoor, wani Ba’amurke kuma lauya mai kare hakkin jama’a wanda a baya ya taba zama lauyan dan jaridan nan da aka kashe Jamal Khashoggi, a cewar wani jami’i da wata kungiyar kare hakkin jama’a da ke da mazauni a Amurka. Wani jami’in gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Asabar cewa, an kama Asim Ghafoor a lokacin da yake wucewa ta filin jirgin saman Dubai a ranar 14 ga watan Yuli bayan an same shi da laifin satar kudi. Wani jami’in Amurka a jiya Asabar ya ce Washington na sane da kamun, amma ba ta iya cewa ko shugaba Joe Biden zai tabo batun a tattaunawar da ya yi da shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa a gefen taron kasashen Larabawa a Saudiyya. Karanta kuma: Saudi Arabiya: Biden zai gana da Yarima Mohammed bin Salman “Babu wata alama da ke nuna cewa tana da alaka da batun Khashoggi,” in ji jami’in na Amurka.
Leave a Reply