Take a fresh look at your lifestyle.

Wani Mai Bidiyon Najeriya TG Omori Ya Bayyana Yadda Zai Chaji Dala Miliyan 1 A Kowane Bidiyo

0 163

Shahararren darektan bidiyon wakokin Najeriya, ThankGod Omori Jesam, wanda aka fi sani da TG Omori ko kuma Boy Director, ya bayyana shirinsa na kara kudinsa zuwa dala miliyan 1 ga kowane hoton bidiyo.

 

Ya bayyana hakan ne a shafin sa na Twitter a ranar Alhamis.

 

Ya ce da zarar ya fara cajin dala miliyan daya a kowane harbi, zai rika harbin bidiyo biyu ne kawai a shekara.

 

Omori ya rubuta, “Da zarar ya kai dala miliyan, Ina buƙatar bidiyo 2 kawai a shekara.”

 

A cewar manema labarai, Davido ya bayyana a watan Maris cewa ya biya TG Omori zunzurutun kudi har Naira miliyan 100 don daukar hoton bidiyon album dinsa na hudu mai suna ‘Timeless’.

 

TG Omori ya kuma tabbatar da karbar kudin faifan bidiyo wanda shi ne mafi tsada a tarihin masana’antar wakokin Najeriya.

 

Sabon Bidiyom bai fiyo kasuwa ba.

Image

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *