Gwamnatin Katsina Ta Samar Da Kwararrun Ma’aikatan Ungozoma A Yankunan Karkara
Kamilu Lawal,Katsina.
Gwamnatin jihar Katsina ta kaddamar da rabon kayan aikin ungozoma ga wasu malaman asibiti da suka samu horo na musamman domin karbar haihuwa da kula da masu juna biyu a yankunan karkara dake jihar
Bikin rabon kayan wanda aka kaddamar a birnin Katsina ya samu halartar masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya hadi da daliban da ake yaye domin gudanar da aikin
Maaikatan ungozomar sama da dari ne da suka samu horon kalkashin wani shirin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da gwamnatin tarayya domin gudanar da aikin a yankunan su daban daban
Shi dai wannan shiri, hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomi ta jihar Katsina ce tayi hadin gwiwa da wani shirin mai taken mata da kiwon lafiya a karkara da ake kira da Women For Health a turance
A kalkashin shirin hadin gwiwar gwamnatin jihar ta dauki nauyin horar da matan samun kwarewa a bangaren karbar haihuwa da nufin kara yawan kwararrun mata ungozoma da ake da su a yankunan jihar
Da yake kaddamar da rabon kayan ga malaman kula da haihuwar, Mataimakin gwamnan jihar Katsina Alhaji Mannir Yakubu ya bayyana cewa samar da kayan aikin na da nufin kara ma ma’aikatan kwarin gwiwa wajen gudanar da aikin karbar haihuwar da kula da masu juna biyun duk lokacin da bukatar hakan ta taso
Yana mai cewa hakan zai samar da nasara a kokarin da ake na inganta kiwon lafiya tare da cimma nasara wajen rage mace macen mata da kananan yara a lokacin haihuwa, musamman ma a yankunan karkara dake jihar
Shima a nasa jawabin a wajen taron, shugaban hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomi na jihar Katsina, Alhaji Usman Maska ya bayyana cewa wadanda suka amfana da horon an zabo su ne daga yankunan kananan hukumomi Talatin da Hudu (34) da jihar take dasu inda suka samu kwarewa a kwalejin horar da aikin ungozoma ta Malumfashi wadda mallakin jihar ce
Kamar yadda ya bayyana bayan da aka yaye su ne gwamnatin jihar ta dauke su aiki tare da tura su a yankunan da suka fito domin cike gibin karancin kwararrun ma’aikatan lafiya da yankunan ke fama dasu
Shugaban hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomin ya kuma bayyana cewa daga kaddamar da shirin a shekara ta 2015 zuwa yanzu, a jihar ta Katsina an horar da rukuni biyar na irin wadannan dalibai tare da daukar su aiki hadi da tura su zuwa yankunan kananan hukumomin jihar
Alhaji Usman Maska wanda ya taya wadanda suka samu horon murna, ya kuma yi fatan za suyi amfani da kayan aikin da aka samar Masu ta hanyar da ta dace domin cimma nasarar da ake bukata.
Leave a Reply