Take a fresh look at your lifestyle.

2023 AFCON: Za a Buga Wasannin Rukuni- Rukuni a ranar 12 ga Oktoba

0 80

Hukumar kula da kwallon kafa ta Afrika ta sanar da ranar 12 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a buga wasannin rukuni-rukuni na gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2023 a kasar Ivory Coast.

 

 

Kwamitin zartaswa na CAF ne ya amince da ranar a taronta da ke birnin Algiers na kasar Aljeriya a ranar Alhamis kuma an sanar da shi ranar Juma’a.

 

 

Sanarwar da CAF ta fitar a ranar Juma’a ta ce “Exco ta sanar da cewa za a gudanar da jadawalin gasar cin kofin Afirka ta 2023 a ranar Alhamis, 12 ga Oktoba, 2023.”

 

 

Masu rike da kofin Senegal da Algeria da Tunisia da Afirka ta Kudu da Morocco da Burkina Faso sun hade da mai masaukin baki ‘The Elephants’ a cikin kungiyoyin da suka samu tikitin shiga gasar da a yanzu aka tabbatar da fara gasar a watan Janairun 2024.

 

 

Najeriya ce ke kan gaba a rukunin A da maki tara a wasanni hudu sannan kuma za ta kara da Saliyo da Sao Tome and Principe a sauran wasanninta biyu na rukuni a wata mai zuwa domin tantance cancantar shiga gasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *