Hajj 2023: Hukumar jin dadin alhazan Jihar Neja ta fara rarraba wa alhazai kayayyaki
Nura Muhammed,Minna.
Hukumar jin dadin alhazan jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta fara rarraba jakunkuna masu daukan kaya kilo 8 da sauran kayayyakin aikin hajji na Maza da Mata ga alhazan jahar.
A wata sanarwa da Jami’in hulda da jama’a na hukumar Malam Hassan Danladi ya fitar ya ce an rarrabawa alhazan kanannan hukumomin Chanchaga da Paikoro da Bosso da Kuma karamar hukumar Rijau.
A cewar Danladi manyan jami’an hukumar ne suka sheda rabon kayayyakin bisa jagorancin Daraktan Mulki na hukumar Hajiya Rukaiya Mohammed Bawa wace ta wakilci shugaban hukumar Muhammad Awwal Aliyu.
Hajiya Rukaiya Mohammed Bawa ta ce za ‘a rarrabawa sauran kananan hukumomin kayayyakin su kafin sukai ga tashi zuwa kasa mai tsarki.
Tun a farkon wannan watan na mayu hukumar jin dadin alhazan jahar Neja ta himmatu wajan ganin ta kammala dukkanin shirye shiryenta a aikin bana.
Har Ila yau hukumar ta kuma gudanar da manyan ayyukan na ganin alhazan jahar Neja sun tashi Kai tsaye daga filin jiragen sama kasa da kasa dake Minna a bana, domin kaucewa shiga rudani kamar yadda aka shiga a bara, inda alhazan suka tashi daga Abuja babban birnin tarayya.
Leave a Reply