Take a fresh look at your lifestyle.

Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Kaddamar Da Sabon Masallacin Majalisar Tarayya

Abdulkarim Rabiu, Abuja

0 136

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kaddamar da sabon masallacin majalisar dokokin kasar.

Sanata Shettima, wanda ya wakilci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci shugabanni a dukkan matakai da su gudanar da ayyukansu bisa tausayin al’umma.

Ya ce masallacin zai inganta ayyukan ma’aikatan majalisar dokokin kasar domin babu wani ma’aikaci da zai fita waje ya nemi masallacin da zai yi sallah.

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, ya yabawa kwamitin tattara kudaden da Sanata Shekarau ya jagoranta.

A cewarsa, ‘yan majalisar da ma’aikatansu sun dora wa kansu nauyin gudanar da aikin ta hanyar tara kudi a kowane wata daga cikin albashinsu , inda ‘yan majalisar dattawa suka ba da gudummawar Naira dubu 400 kowane, yayin da Yan Majalisar Wakilai suka bada Naira dubu 250 a kowane wata na tsawon watanni biyar.

Kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya jaddada muhimmancin sadaukar da dukiya da karfi da lokaci wajen bautar Allah da taimakon bil’adama.

Mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero wanda ya wakilci Sarkin Musulmi ya bukaci kwamitin da ya tabbatar da ganin an gudanar da kula masallacin yadda ya kamata.

Shugaban kwamitin kula da ayyukan masallacin Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa an gina masallacin ne ta hanyar gudunmawar da ‘yan majalisa musulmai da ma’aikatan majalisar dokokin kasar suka bayar inda aka tara Naira miliyan 570.

An Kuma gudanar da Sallar Juma’a karkashin jagorancin Babban Limamin Masallacin Sheikh Rayyanu Sani.

Abdulkarim Rabiu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *