Take a fresh look at your lifestyle.

Hawan Keke Na Inganta Lafiyar Dan Adam- Inji Likita

30

Babban Likita, Dokta Tunji Akintade, ya shawarci ‘yan Najeriya da su Rika Hawan domin inganta lafiyar jikinsu da jin dadin su. Ya ba da wannan shawarar ne a wata hira da manema labarai a Legas yayin wani taron tunawa da ranar kekuna ta duniya ta 2023. Ana bikin ranar kekuna ta duniya kowace shekara a ranar 3 ga watan Yuni domin karfafawa mutane gwiwa su zabi kekuna a matsayin hanyar sufuri da kuma rage cunkoson ababen hawa, burbushin mai, da hayakin Carbon tare da inganta lafiya da walwala. Taken ranar Kekuna ta Duniya 2023 ita ce, ‘Hawa Tare don Dorewar makoma’.

 

 

KU KARANTA KUMA: Ranar Kekuna ta Duniya: Hukumar FRSC ta bukaci ‘yan Najeriya su rika amfani da keken hawa

 

 

Dokta, Akintade ya bayyana cewa inganta hawan keke a Najeriya yana da matukar muhimmanci wajen rage yawan cututtuka da ba sa yaduwa kamar hauhawar jini, ciwon suga, da rage gurbatar iska da hayaniya.

 

 

A cewar shi, rungumar kekuna a matsayin hanyar sufuri na da matukar muhimmanci a halin yanzu domin da yawa daga cikin ‘yan kasar na kokawa da kalubalen da karin farashin man fetur ke haifarwa da kuma tsadar sufuri da ke tasowa sakamakon cire tallafin man fetur.

 

 

Ya ce, “tuka keken  hawa ya dace, yanzu da ‘yan Najeriya ke fama da matsalar man fetur domin hakan zai taimaka wajen tsimin kudi da kuma samun lafiya. Mutane da yawa ba sa motsa jiki. Tukin keke da safe da maraice yana da kyau don rage haɗarin cututtukan da ba sa yaduwa.

Maimakon mu tuka motoci zuwa kasuwa ko ziyarci abokai a unguwarmu, za mu iya amfani da kekuna. hawan keke na iya taimakawa inganta lafiyar zuciya da jijiyoyin jini, huhu, da lafiyar hankali. Hanya ce mai daɗi don kasancewa cikin koshin lafiya saboda yana taimaka muku rage nauyi, rage ƙwayar cholesterol da ƙarfafa ƙafafu, ”in ji shi.

 

 

Likitan ya ce baya ga fa’idar kiwon lafiya, hawan keke kuma na iya taimakawa wajen rage cunkoson ababen hawa, gurbatar iska, inganta lafiyar jama’a da samar da muhalli mai tsafta.

 

 

Ya kuma shawarci masu keken hawa da su ba da fifikon tsaron lafiyar su ta hanyar kawata kayan kariya da kuma bin ka’idojin zirga-zirga. Ya kuma yi gargadi game da hawan keke a manyan tituna domin gujewa hadurra.

 

 

Dokta Akintade ya kuma yi kira ga gwamnati da ta inganta hawan keke ta hanyar samar da tsayayyen hanyoyin tuka keke da tafiya da fitilun titi da inganta tsaro domin inganta tsaro.

Comments are closed.