Take a fresh look at your lifestyle.

Arsenal Suna Martin Odegaard A Matsayin Kyaftin Kulab

0 400

Arsenal ta sanar da cewa dan wasan kasar Norway Martin Odegaard ne sabon kyaftin din kungiyar. Gunners din ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na yanar gizo ranar Asabar. Odegaard ya koma Arsenal ne daga Real Madrid a shekarar 2021 a lokacin kasuwar musayar ‘yan wasa ta watan Janairu kafin yarjejeniyar ta zama dindindin. Sanarwar ta arsenal.com ta ce: “Mun yi farin cikin sanar da cewa an nada Martin Odegaard a matsayin sabon kyaftin din kungiyar maza ta farko. “Dan wasan mai shekaru 23 ya taka rawar gani tun lokacin da ya isa filin wasa na Emirates daga Real Madrid a watan Janairun 2021, a matsayin aro, kuma ya ci gaba da buga wasa sau 60, inda ya ci kwallaye tara. “Odegaard yana da gogewa na sanya rigar hannu, kasancewar ya kasance kyaftin din Norway tun a watan Maris na 2021, wanda ya lashe wasanni 43. “Muna yiwa Martin fatan alheri a matsayin kyaftin din mu.”

Aliyu Bello, Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *