Take a fresh look at your lifestyle.

GWAMNAN KANO YA KADDAMAR DA AIKIN KULA DA MASU LARURAR ZUCIYA

Yusuf Bala Nayaya,Kano.

0 101

Gwamnan jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya ya kaddamar da aikin kula da masu larurar zuciya ko fidar zuciya, aikin da ke zama kyauta da gwamnatin kasar Saudiyya ta dauki nauyi da hadin gwiwar kungiyar hadakar Musulmi ta duniya da Asibitin Malam Aminu Kano (AKTH). An dai kaddamar da aikin ne a dakin taro na asibitin na AKTH.

 

Da yake kaddamar da aikin kula da masu cutar da ta shafi zuciyar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na hada gwiwa da kungiyoyi masu zaman kansu da daidaikun mutane da masu taimakon al’umma da ke son tallafawa wajen samar da horo ga maaikatan lafiya da ma tallafa wa marasa lafiyar.

 

Gwamnan Injiniya Abba Kabir ya bayyana farincikinsa da wannan aiki da yace zai taimaka wa gwamnatin jihar ta Kano kan muradin da ta sa a gaba na ba da kulawar da ta dace ga fannin na lafiya.

 

 “Mun yi matukar farinciki da yadda kuka zo Kano don ba da wannan muhimmin taimako. Jihar Kano jiha ce mafi yawan jama’a a Najeriya da yawan al’ummar da suka haure miliyan 21. Muna da matane da suke matukar bukatar tallafi wadanda basu da iko na iya kula da lafiyarsu .” A cewar gwamnan.

 

Ya kara da cewa “za mu mayar da hankali kan alkawuran da muka yi wa al’umma na samar da manyan asibitoci a kananan hukumomi 44 na jihar da samar da cibiyar kula da lafiya a matakin farko da sake maido da asibitoci na tafi da gidanka don mutanen da ke zaune a yankunan karkara wadanda ke neman kulawar lafiya kyauta.”

 

Jagoran tawagar daga kasar Saudiyya Dakta Utman Al-uthman Saad ya ce cikin tawagar tasu akwai kwararrun likitocin zuciya 20 wadanda za su yi aikin fida kuma za su yi aiki tukuru don cimma burinsu.

 

Shima a nasa martini shugaban asibitin koyarwar na Aminu Kano Farfesa Abdulrahman Abba Sheshe ya ce kwararrun sun zo a lokacin da ya dace ganin yadda ake kara samun masu cutar zuciya dalilin karuwar masu hawan jini a Arewacin Najeriya.

 

Shugaban asibitin ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta zo da tsare-tsare da za su farfado da fannin na lafiya, abin da zai hana yawaitar masu balaguro zuwa kasashen ketare don duba lafiyarsu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *