Take a fresh look at your lifestyle.

Harin Otal a Mogadishu na Somalia ya kashe mutane shida

0 90

Akalla fararen hula shida ne suka mutu yayin da wasu 10 suka jikkata a wani kawanya na tsawon sa’o’i shida da mayakan kungiyar al-Shabab suka yi a wani otal da ke bakin teku a Mogadishu babban birnin Somalia, in ji ‘yan sanda a ranar Asabar.

 

“Jaruman jami’an tsaro uku ne suka yi shahada yayin aikin ceto,” in ji rundunar ‘yan sandan Somaliya a cikin wata sanarwa.

 

Sanarwar ta kara da cewa, jami’an tsaro sun kashe maharan bakwai daga kungiyar ‘yan tawayen da ke da alaka da al-Qaeda.

 

An kai harin ne da yammacin ranar Juma’a a wani shahararren kantin sayar da abinci na Pearl, da ke gabar tekun Liido, babban birnin kasar.

 

“Dakarun tsaro sun yi nasarar kashe ‘yan ta’addar #Alshabaab da suka kai harin ta’addanci a Otal din Pearl Beach da ke gabar tekun Lido, #Mogadishu,” a cewar kamfanin dillancin labarai na kasar Somalia SONNA a shafin Twitter.

 

“An ceto fararen hula da dama yayin aikin,” in ji SONNA.

 

A baya kamfanin dillancin labaran ya wallafa hotuna da ke nuna sojoji a cikin gidan cin abinci na otal din suna mayar da martani kan harin. Daya tsaya kusa da wata kofa ta gilas dauke da bullet a cikinta, sai takalmi da kwandon kura a kusa da shi.

 

Kungiyar Al-Shabab ta dauki alhakin kai harin.

 

Shaidu sun bayar da rahoton jin karar fashewar wani abu da ya biyo bayan harbin bindiga a otal din.

 

Hare-haren dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da mayakan Al-Shabab suka kashe dakarun wanzar da zaman lafiya na Uganda 54 a wani hari da suka kai a sansanin dakarun Tarayyar Afirka da ke garin Bulo Marer a kudancin kasar a watan jiya.

 

Ci gaba da Hare-hare

 

An kori Al-Shabab daga manyan garuruwa da biranen Somaliya amma ta ci gaba da rike madafun iko a yankunan karkara, kuma ta ci gaba da kai hare-hare kan tsaro da fararen hula ciki har da babban birnin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *