Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Jiha Neija ya bukaci alhazan jihar su kasance jakadu na gari

Nura Muhammed,Minna.

0 104

An bukaci alhazan jahar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya da su kasance jakadu na gari a yayin zaman su a kasa Mai tsarki.

 

 

Gwamnan jahar Umar Muhammad Bago shine ya bukaci hakan a lokacin da yake yiwa maniyatan jawabin bankwana kafin tashin su zuwa Saudiya.

 

 

Gwamnan Wanda mataimakin sa Comrade Yakubu Garba ya wakilta ya ce jahar zata yi alfahari da  alhazan middin suka kare mutuncin su da na jahar da ma kasa baki daya.

 

 

Hakazalika Gwamnan ya bukaci su da su kasance masu taimakawa juna  da yi hakuri da Kuma yiwa kasa addu’oin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali musammanma ganin irin kalubalen da take fuskanta a halin yanzun.

 

 

Gwamna Umar Muhammad Bago ya kuma baiwa maniyatan hakuri na  rashin tashin su daga Minna wanda hakan ya faru ne sakamakon gyare gyaren da ake yi a filin jirgin saman Minna.

 

 

A jawabin sa Shugaban hukumar jin dadin alhazan jahar Malam Muhammad Awwal Aliyu ya yabawa Gwamnan bisa hadin kan da yake basu sannan ya godewa Allah bisa nasara samun kammala dukkanin shirye shirye da Yakamata daga bangaran hukumar.

 

 

Malam Abusufyan shine babban jami’in hukumar a karamar hukumar Chanchaga ya ce sun yi iyakar kokarin su na ganin alhazan sun tashi a Minna, amma  hakar su bata cimma ruwa ba, sai dai ya ce hukumar zata ciga da aiki tukuru domin ganin sun  sauka a filin jirgin saman Minna bayan kammala aikin hajjin.

 

 

“Muna fatan hakan ya sa alheri ne a gare mu da ma alhazan, Amma in Sha Allah zasu sauka da Kayayyakin su bayan kammala aikin hajjin.”

 

 

Maniyata dari uku da talatin da biyar (335) Maza da Mata ne da suka fito daga kanannan hukumomin Mariga da Chanchaga da Kuma Mashegu ne suka tashi daga filin jirgin saman Abuja zuwa Madinatul Munawwara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *