Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, an soke ganawar da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na kasar Japan suka yi a gefen kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya da na ASEAN a Cambodia.
A cewar mai magana da yawun ma’aikatar, Hua Chunying ta ce, bangaren kasar Sin ya nuna rashin jin dadinsa matuka da sanarwar hadin gwiwa da rukunin kasashe bakwai suka fitar game da Taiwan.
Ministocin harkokin wajen kasashen G7 da suka hada da Japan sun yi kira ga kasar Sin a ranar Laraba da ta warware rikici a mashigin tekun Taiwan cikin lumana.
Leave a Reply